Connect with us

LABARAI

An Cafke Matashi Mai Garkuwa Da Mutane A Legas

Published

on

An gabatar da wani matashi dan shekara 26 mai suna Salomon Ojo a gaban wata Kotu dake Jihar Legas bisa zargin yin garkuwa da mutane uku. Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ba da rahoto cewa ana dai duhumar Ojo ne da laifuffuka guda biyu, laifin hadin kai da ‘yan ta’adda da kuma laifin yin garkuwa da mutane inda duka ya karyata.

Lauya mai kara, Sajan Maria Dauda ta bayyana cewa shi dai wanda ake zargi ya aikata laifin ne ranar 5 ga watan Satumba a kan layin Irepodun cikin karamar hukumar Igando dake Jihar Legas. Ta kara da cewa Ojo ya yi garkuwa da Osahan Obazee dan shekara 22 da Augustine Ekwegbudu dan shekara 27 da kuma Fadugbabe Akindele mai shekaru 29. Laifin dai ya saba wa sashi na 2 zuwa na uku na kundin tsarin mulkin Jihar Legas ta shekara 2017.

Alkali mai shari’a Mista A.O. Salawu ya ba da belin wanda ake zargi kan kudi 200,000 tare da mutane biyu sannan an daga sauraran shari’ar har sai zuwa ranar 11 ga watan Oktoba.

A bangare daya kuma, wata mata ‘yar shekara 29 mai suna Cecilia Adejoh ta bayyana a gaban wata Kotu bisa zargin satan waya ranar Juma’a.

Lauya ‘yan sanda Mista Theophilus Chukwuma ta bayyana wa Kotu cewa wani mutum mai suna Lawani John ne ya kawo rahoto ofishin ‘yan sanda dake Garki ranar 26 ga watan Agusta. Chukwuma ya kara da cewa ana zargin Adejoh ranar 25 ga watan Agusta a otal din Rita Lori dake Garki, lokacin da ta ce za ta bi John zuwa gidansa.

“Yayin da suka isa gidan, sai ta yi awan gaba da wayarsa kiran Techno H7 wanda kudin sa ya kai kamanin naira 48,” inji Chukwuma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: