Daga Yusuf Shu’aibu
Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana cewa luguden wutar da take yi wa ‘yan bindiga a shiyyar arewa maso yamma tana haifar da kyakkyawan sakamako, inda ta bayyana cewa ruwan bamabaman da take yi wa miyagun ya karya lagonsu.
Babban jami’i mai kula da sashen yada labarai na shalkwatar tsaron kasa, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana haka ga ‘yan jarida a Abuja, yayin gudanar da taron manema labarai na mako-mako kan ayyukan da dakarun sojin kasar nan ke aiwatarwa, inda na wannan makon ya kunshi bayanan nasarar da aka samu kan harkokin tsaro a tsakanin 19 zuwa 25 ga Nuwambar 2020.
Ya kara da cewa, ‘yan sandan ciki masu kula da shiyyar Katsina ne suka samu nasarar cafke ma’auratan a wani kauye da ake kira Abukur, dauke da albarusai da nufin shigar da su garin Katsina. Albarusan kamar yadda Enenche ya bayyana, sun kunshi magazin guda 14, da tuntun jigida guda 61 masu samfurin 9.6mm da wasu kunshin albarusan guda 399 samfurin 7.62mm.
Har ila yau, shalkwatar tsaro ta Nijeriya ta bayyana cewa, an kusan kawo karshen ta’addanci da tayar da kayar baya a Nijeriya nan ba da dadewa ba, bayan da aka shelanta yin aiki ba dare ba rana.
Ta kara da cewa, sakamakon samar da wannan sabon sintiri da aka yi, ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya suka fara raguwa. Ta ce, an gudanar da sintiri masu yawa a wannan kwanaki.
Ya ce, rundunar sojoji masu gudanar da sintiri na “Troops of Operation Hadarin daji” a yankin Arewa-Maso- Yamma, sun gudanar da sintiri masu yawa a yankin Arewa- Maso – Yammacin kasar nan wanda suka yi nasarar tatattakan ‘yan ta’adda da dama.
“A ranar 21 ga watan Nuwambar shekarar 2020, rundunar sojojin “Operation ACCORD” ta gudanar da wani samame a kauyen Galadi da ke karamar hukumar Shinkafi cikin Jihar Zamfara wanda ya yi sanadiyar damke ‘yan bindiga guda biyu tare da kwato makamai kirar AK-47 guda biyu.
“A wani farmakin na daban wanda ya guda a ranar 21 ga watan Nuwambar shekarar 2020, rundunar sojojin sun gudanar da wani samame a kauyen Gobirawa wanda ya yi sanadiyyar fatattakan ‘yan bindiga. A lokacin wannan samame, an samu kama ‘yan bindiga guda shida tare da bindigogi kirar AK 47 guda hudu da bindigar toka guda uku da kuma babura guda biyu daga hannun ‘yan ta’addan.
“A ranar 24 ga watan Nuwambar shekarar 2020, rundunar sojojin ta gudanar da wani sintiri na musamman wanda ya yi sanadiyyar cafke mutum uku da ake zargi da satar shanu guda 3,000. Wadanda ake zargin sun amince da laifukansu. A wannan rana kuma, an samu nasarar damke ‘yan bindiga guda biyu a kauyen Tsayau da ke karamar hukumar Jibia cikin Jihar Katsina, sakamakon samamen hadin gwiwa a tsakanin rundunar sojojin da ke aiki a Katsina da kuma na Gurbin Baure. Wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.