Idris Aliyu Daudawa" />

An Cafke Mutane 19 Suna Kokarin Kona Ofishin ‘Yan Sanda A Legas

Mataimakin

Rundunar ‘yansanda ta jihar Legas ta gurfanar da mutane 19 wadanda ake zargin su da kokarin su kona ofishin ‘yansanda na Ejigbo da misalin karfe goma sha daya da kwata na dare (11.15pm) ranar Asabar.
Wani mazauni unguwar da kawaia ana kiran shi da suna Tunde ya bayyana cewar, yana zaune shi daya lokacin da yaga daruruwa ‘yan Okada suna dauke da munanan makamai, suna kokarin su nutsa kansu zuwa ofishin ‘yansanda.
Kamar dai yadda ya bayyana bai san abin da suke cewa ba, har sai lokacin da abokin shi ya bashi labarin cewar motar ‘yansanda ta kashe wasu daga cikin ‘yan’uwansu.
Ya ci gaba da bayanin cewar ‘yan mintuna kadan kuma lokacin da su ‘yan Okada suka fara jefe- jefen duwatsu zuwa ofishin ‘yansanda, har ma suka yi barazanar kona ofishin ‘yansanda. Ya ci gaba da bayanin cewar ana cikin wannan halin halin ne, har suka samu damu damar lalata motocin ‘yansanda.
Tunde ya kara jaddada cewar lokacin da ‘yansanda suka kara shiri, na murkushe kokarin da ake yi na caji -ofis na ‘yansanda, wasu daga cikin ‘yan Okadan sun samu raunuka daban- daban.
Ya kara bayanin cewar “Ina zaune sai naga daruruwan matasa suna gudu zuwa ofishin ‘yansanda na Ejigbo, suna magana ne cikin kalmar Hausa, don haka ni ban san ma abin da suke cewa ba.
“ Amma na tambayi daya daga cikin su wanda kuma abokina ne ko ya san abin da yake faruwa? sai ya bada amsar cewar wasu ‘yansanda ne suka kashe masu ‘yanuwansu biyu, sun kuma zo ne saboda su yi ramuwar gaiya.”
Mai magana da yawun ‘yansandak na jihar Legas ko kuma jami’in hulda da jama’a babban safuritenda na ‘yansanda (CSP) Chike Oti, ya nuna rashin jin dadin shi dangne da shi wannan harin da aka kai.
Kamar dai yadda ya ce dokar jihar Legas mai kula da abubuwan hawa ta hana duk wani dan Okada yin aiki bayan karfe goma na dar ya yi (10pm).
Ya ci gaba bayanin cewar su ‘yan Okadan sun yi kokakrin kona caji -ofis na ‘yansanda dake Ejigbo, amma sai aka yi sa’a an dauki matakai masu tsauri cikin sauri.
Oti uya kara jaddada cewar ‘yansanda sun yi sa’ar mukushe kokarin su matasan, inada kunmasuka yi amfani da Barkonon tsohuwa (firing tear gas canisters) saboda su tarwatsa su matasan masu son kawo tashin hankali, amma babu wanda aka harba
Shi jami’in hulda da jama’a na rundunar (PPRO) ya bayyana cewar,“ Da gangan su ’yan Okadan suka lalata motoci biyu wadanda kuma na aiki ne, mallakar bangaren Rapid Response Skuad, ko kuma wadanda suke kai wani taimako na gaggawa wadanda suke Ikeja. Amma ‘yan sanda babu wanda suka harba, sun harba barkonon tsohuwa ne, kawai saboda su tarwatsa su. Sai dai kuma ‘yansanda sun kama mutane goma sha tara (19) a kokarin da suke na kona caji -ofis na ‘yansanda.
“ Dansanda wanda yake gadi da dare ya ga wasu mutane suna kokarin zuwa, daga nan ne fa sai kowa ya shirya, saboda an fara tunanin me ya sa su wadannan mutanen suke kokarin zuwa caji- ofis na ‘yansanda a wannan lokacin.
“ Yan mitoci kadan sai kuma ita tawagar ta fara jefe jefen duwatsu da wasu abubuwa zuwa caji –ofis na ‘yansanda, amma kuma sai su ‘yansanda suka yi kokari wajen hana su shiga cikin ofishin nasu, amma idan da an basu dama, da yanzu sai dai a rika maganar cewar an kona caji -ofis na ‘.
“ Amma duk da hakan ta kokarin da suke yi na su samu kutsawa cikn caji ofis na ‘yansanda, sun samu damar lalata motoci biyu, wadanda aka ajiye su a waje. Shi mai kula da wannan ofishin na ‘yansandaThe DPO ya sami wata tawaga wadda tayi amfani dea barkonon tsohuwa wajen tarwatsa su, saboda a kauce ma duk wani abin da zai sanadiyar mutuwar wani.”
A wani ci gaba kuma da aka samu su ‘yan tawagar ‘yan sanda masu kai farmakin babu masaniya, sun samu sa’ar kama Shugaban tawagar mutanen hudu, mai suna Osuji Chibuzor, mai shekaru 42, saboda samun shi da aka yi da laifin da cutar wata mata mai shekaru 34 kudaden da suka kai Naira 165,000.
An dai samun labarin cewar shi wanda ake zargi da aikata laifin, yana yin harkokin na shiu ne akan hanyoyin Ikeja, Ojota, Ojodu Berger, Ogba, hanyar zuwa Kwalej da kuma Agege Agege, ya yin da kuam ofisoshin su suna a layi na 8 Afolabi Iju Shaga da kuma layi na 7 Salami Oko-Oba, Agege.
Shi dai Chibuzor rawar daya taka kamar dai yadda tawagar ‘yan sanda ta RRS, shi yana daukar hankalin mutane ne, wajen yin karaya da karerayi, wannan kuma yana yin hakan ne, sai bayan da yaga cewar sun riga sun sakan kance da al’amarin.
Shi wanda ake zargi da aikata laifin ya bayyana cewar ‘yan tawagar shi, sun aba mutrane wadanda suka samu shiga cikin komar su, suna kuma amfani ne da dala wadda take jabu ce, saboda su ja ra’ayin su.
Ya ci gaba da bayanin cewar wasu daga cikin ‘yan tawagar sun hada da Frank, Stella da kuma Emeka, inda kuma ya kara bayyana cewar, su kan bi ta hanyoyin Ikeja, Ojota da kuma Agege, ko wacce rana, saboda su jawo hankalin mutane zuwa ofisoshin nasu guda biyu.
Kamar dai yadda ya ci gaba da yin bayani su kan rudi su mutanen da suka samu ta hanyar hada- hadar dalar Amurka.
Chibuzor ya kara bayanin cewar bayan sun kawo mutane zuwa ofisoshin nasu, sai su ‘yan tawagar su yi amfani da Pastor (Fasto) wanda shine zai yi ma mutanen ko kuma duk mutumin daya shiga hannun su, addu’a irin ta kirista.
Bugu da kari kuma a dai dai lokacin da ake yi ma su mutanen addu’a sai kuma a bukaci cewar, su kawo kuadade saboda za’a sayi wani mai mai suna (anointing oil) nko kuma wani sinadarin kimiyya na ruw, weanda za’ayi amfani da shi wajen wanke kudade, da kuma sauran wasu ayyuka.
Shi dai wanda ake zargi da aikata laifin ya bayyana cewar wani shiga halin da bai gane bane ya say a shiga ya shiga cikin ita kungiyar, shekaru uku wadanda suka wuce.
Ya dai kara bayanin cewar, “ Duk da yake dai da akwai sauran wasu ‘yan kungiyoyin damfara masu yawa a Legas, wadanda kuma suna zaman kansu ne, amma kamar yadda ya bayyana “Mu hudu ne kawai muka hada wannan tawagar tamu. Muna kuma kuma yin ayyukan namu ne a Agege, Ogba, hanyar kwaleji ,Ojodu Berger, Ojota, Ikeja, Alausa da kuma Ifako-Ijaiye”.
“Abin da na amsa daga wurin ita yarinyar Naira N120, 000, na kuma san abokan harka ta sun cire Naira N45, 000 daga cikin asusun ajiyarta, wajen amfani da katin ta na cire kudi (ATM card). A shirye kuma nake na maida mata dukkan kudaden ta da na amsa.”
Ita dai matar da bata son a ambaci sunan ta ba, ta bayyana cewar ta shiga mota ne zuwa Ojota da Ojodu Berger, inda ta ci gaba da bayanin cewar tana Oregun ne, lokacin da shi direban ya dauke ta, a matsayin ita fasinja ce.
Ta ci gaba da bayanin cewar ita bata san ma yadda aka yi ba ta samu kanta a Iju ba, maimakon Ojodu Berger.
Bayanin nata ya nuna cewar su ‘yan tawagar sun sa tayi rantsuwa da cewar ba zata taba fadi ma wani ba, akan al’amarin da yake tsakanin ta da su ‘yan tawagar.
Wadda abin ya rutsa da ita an ji tana cewar, “Ai har yanzu muna cikin Oregun ne inda direba ya dauke wani fasinja, inda daga wancan lokacin ne kuma suka fara yi mata wasa da hankali.
Ta ci gaba da bayanin“Na dai kasance a ofishin su ne, a Iju, inda suk aamshi dukkan kudade na, har na dana cikin asusun ajiya ta. Sun san ya ni na yi rantsuwa cewar kada in fada ma kowa abin da ke tsakanin mu. Daga nan kuma sai sai suka ce mani ko za su sake samun wasu Naira N60, 000 saboda ko a samu a kammala shi aikin.
“Bayan suna mshi Naira 165,000, duk dfa hakan suna bukatar na kara masu, daga nan sai na samu rance Naira N60, 000, wanda cikon kudaden da suke so ne daga wuri na, ina kan hanya ta ne ta kai masu sauran lokacin da hankali na ya dawo mani sosai.
“ Sai ga shi Allah ya taimaka mani tare da hadin kan taimakon jami’an RRS, da haka ne na ja hankalin (Chibuzor) har aka samu kama shi.”
Shi kuma kwamishinan ‘yansanda na jihar Legas, Zubairu Mu’azu, ya yi kira da jami’an ‘ynasanda da suyi kokari su kori irin wadannan bata garin daga jihar Legas, musamman ma a wuraren da suka yi badin suna’.

Exit mobile version