Yusuf Shuaibu" />

An Cafke Mutum 21 A Wani Rikicin ’Yan Kungiyar Asiri A Ikorodu

An cafke mutum 21 wadanda a ke zargin mambobin ‘yan kungiyar asiri ne masu hamayya da juna na Eiye da Aiye Confraternities, a garin Ikorodu da ke Jihar Legas, bayan wani arangama wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu. Wata majiya ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya cewa, makamai daban-daban wadanda su ka hada da, bindigogi, adduna da kuma gatari, su ne ‘yan kungiyar su ka yi amfani da su wajen rikicin, wanda ya afku a yankunan Isikalu da Solomade da ke cikin garin Ikorodu, inda su ka tada hankulan mutanen yankin. An bayyana cewa, sakamakon arangamar wanda ya fara tun daga ranar Alhamis har zuwa ranar Juma’a, da yawa daga cikin mutunen yankin sun kasa zuwa aiki, ko kuma bude shagunansu har sai da rundunar ‘yan sanda masu yaki da ‘yan kungiyar asiri wanda kwamanda CSP Uduak Udom ya ke jagoranta su ka isa wurin da lamarin ya faru.

“Hankula sun kwanta a yankin tun lokacin da ‘yan sanda su ka isa wurin, yayin da a ka cafke mutum 21 wadanda a ke zargi, domin gudanar da bincike. “Wadanda a ka cafke su na taimaka wa ‘yan sanda da bayanai game da ayyukan kungiyar asiri, musamma ma a yankin Ikorodu,” in ji majiyar.   

Lokacin da a ka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da wannan kamen, ya bayyana cewa, a cikin wadanda ‘yan sanda su ka cafke har da shugaban ‘yan kungiyar asiriwanda a ke ta nema ruwa a jallo. A cewar Elkana, da misalin karfe 10 na dare ne, ‘yan sanda su ka samu bayanai cewa, ‘yan kugiyar asiri su na gwabzawa a yakunan Isikalu da Solomade da ke cikin yankin Ikorodu. Nan take tawagar ‘yan sanda masu yaki da ayyuakan kungiyar asiri su ka isa yankin.

A cewarsa, an samu nasarar cafke shugaban daya kungiyar mai suna Yusuf Omidele, wanda a ke yi wa lakabi da General, wanda a ke nema ruwa a jallo a cikin mutum 20 da a ka kama. “An Sha gurfanar da General a gaban kotu, inda a ke yanke masa hukuncin zama a gidan yari. Ya kammala hukuncin da a ka yanke masa a shekarar 2014, inda a yanzu ya zama shugaban kungiyar asiri na Eiye Confraternity. “Ya jagoranci farmakin da a ka kai wa mambobin kungiyar asiri na Aiye Confratanity, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar matar shugaban kungiyar a cikin makon da ya gabata.

“Dukka wadanda a ka cafke mambobin kungiyar asiri ne na Aiye da Eiye Confraternity, kuma dukkan su sun amsa cewa, sun  ‘yan kungiyar asiri ne. Mutum biyu  ‘yan kungiyar asiri sun mutu, yayin da shida su ka samu raunika a wannan arangamar. “Rundunar  ‘yan sanda za ta cigaban da akkamar da sintiri a yankin, har sai ta  samu  nasarar cafkke sauyan mambobin kungiyar wadanda su ka gudu. “An kwato karamar bindiigar hannu kirar gida  guda hudu, adduna guda takwas da kuma gatari guda uku daga hannun wadanda a ke zargi,” in ji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ya bayyana cewa, kwamishinan ‘yan sandar Jihar Legas, Mista Zubairu Muazu, ya gana da masu ruwa da tsaki na jihar, wajen yadda za a samu nasarar dakile ayyukan ‘yan kungiyar asiri a jihar, musammam ma a yankin Ikorodu. Ya kara da cewa, ya nemi goyan bayan su, domin yakar ayyukan ‘yan kungiyar asiri a yankin Ikorodu.

Kamfanin dillancin da labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, an samu wani arangamar ‘yan kungiyar asiri a yankin Iponri da ke cikin garin Surulere, a ranar Laraba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Azu. Ya kara da cewa, mambobin kungiyar sun gwabza fada a yankin Ike-Olu da ke yankin Iponri har sai da su ka shirya kansu.

Exit mobile version