Muhammad Maitela" />

An Cafke Mutum Hudu Bisa Zargin Yi Wa Yara Fyade A Yobe

Fyade

Ranar Litinin rundunar yan-sanda a jihar Yobe ta sanar da ta cabke mutum hudu wadanda ta ke zargi da taron- dangi wajen yi wa kananan yara mata fyade a jihar.

Rundunar ta bayyana hakan ta hannun jami’in hulda da jama’a, ASP Dungus Abdulkarim, a zantawarsa da manema labarai Damaturun jihar Yobe.
Ya bayyana cewa mutane ukun da ake zargi da aikata fyaden su ne Musa Mohammed, dan shekara 25, Mohammed Dahiru shekaru 27, hadi da Adamu Saidu dan shekara 46 a duniya, wadanda su ka shiga hannun jami’an su da ke aiki a ofishin yan-sandan yanki da ke Potiskum ranar 25 ga watan Disamba, tare da zargin sun yi wa yar shekaru 13 fyaden.
Abdulkarim ya kara da cewa wadanda ake zargi da aikata laifin zu yi amfani da hutun ranar bikin kirsimeti ta hanyar yaudarar yarinyar wajen shigar da ita makarantar Brema Primary a garin, wajen aikata masha’a da ita.
Bugu da kari kuma, ranar 26 ga watan Disamba, ofishin yan-sandan yanki da ke Geidam ta cabke Bako Umaru dan kimanin shekara 35, da zargin sace yarinya yar kimanin 11 tare da yi mata fyade a unguwar Hausari, wanda sakamakon hakan ta samu raunuka a al’aurarta.
Jami’in hulda da jama’ar ya ce saboda yadda jininta ya zuba a raunin da yarinyar ta samu, ya sanya an kwantar da ita wata asibitin da rundunar ba ta bayyana ba a birnin Damaturu- sakamakon abka mata da mai laifin ya yi.
Har wala yau, ya kara da bayyana cewa, ranar 27 ga watan, jami’ansu na ofishin yan-sandan yanki a Gashuwa sun kama Mohammed Jajere da zargin yi wa wata mace mai danyen goyo fyade a kauyen Garindalal na gundumar Dagona.
Ya ce, wanda ake zargin, Jajere ya abka wa matar a daidai lokacin da take kokarin murmurewa a sabuwar haihuwa, sa’ilin da ya tsallaka gidan a yunkurin yin sata.
Haka zalika, ya ce rundunar su ta na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin tare da gabatar da wadanda take zargi da aikata laifukan da zarar ta kammala aikinta.
A hannu guda, wannan matsala ta fyade ta na nema ta zama ruwan dare musamman ga kananan yara a jihar.
ASP Abdulkarim ya sanar da cewa a cikin watan Disamba kadai, sun samu korafe-korafen zargin fyade guda tara ga kananan yara, daga bangarori daban-daban na jihar Yobe.
Saboda wannan ne jami’in hulda da jama’a na rundunar yan-sandan jihar Yobe ya bukaci samun cikakken goyon bayan jama’a wajen sanya ido tare da kwarmata mu su bayanan masu aikata manyan laifuka.

Exit mobile version