Rundunar ‘yan sandar jihar Ogun ta cafke wani boka mai suna Jamiu Olasheu dan shekara 35 tare da wasu mutum uku, bisa samun su da kokon kai. An bayyana cewa ‘yan sanda da ke gudanar da aiki a yankin Agbara su ne suka cafke mutum biyu wadanda suke kan babur a Kofedoti cikin garin Agbara. Lokacin da aka caje mutanen Teslim Ayeniromo dan shekara 45 da kuma Sunday Kolade mai shekaru 35, sai aka samu kokon kan a cikin buhu.
Da yake tabbatar da kamen, kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Abimbola Oyeyemi ya bayyana cewa, nan take aka cafke mutum biyun sannan aka garzaya da su zuwa shalkwatar ofishin ‘yan sanda da ke Agbara, inda DPO Adegbite Omotayo yake gudanar da binciken lamarin.
Oyeyemi ya kara da cewa, bisa bincike da aka gabatar ya nuna cewa, wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa wani mutum mai suna Michael Osanyinbi dan shekara 51, shi ne ya ba su wannan kokan kan domin su kai wa boka. Wadanda ake zargin sun jagoranci DPO zuwa gidan mutumin tare da bokan wanda za a bai wa kokon kan, ‘yan sanda sun cafke dukkanin su. Oyeyemi ya ce, “Bokan ya yi bayani inda yake cewa shi ne ya bukaci wannan kokon kai, Michael Osanyinbi ya yi alkawarin zai ba da naira 25,000 tare naira 1,000 kudin babar ga wadanda za su samo wannan kokon kai. Ya kara da cewa, ya bukaci wannan kokon kai ne domin a yi tsafi da shi.
A halin yanzu dai, kwamishinan ‘yan sandar jihar Ahmed Iliyasu ya bayar da umurnin a yi gaggawar mika wadanda ake zargi zuwa sashin rundunar ‘yan sanda masu binciken manyan laifuka domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da su a gaban shari’a.”