Daga Khalid Idris Doya
‘Yan sanda sun samu nasarar cafke mutum uku bisa zarginsu da hannu a kai hari Majami’ar cocin mahaifin gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike wato ‘Christian Unibersal Church International’.
Kakakin rudunar Nnamdi Omoni, ya shaida cewar wadanda suke zargin su na taimaka musu wajen zurfafa bincike.
A karshe mako da daddare ne dai wasu ‘yan daba da yawansu ya zarce biyar suka shiga cikin majami’ar cocin ‘CUCI’ da ke layin 25 Azikiwe Street Mile, 3 Diobu, inda suka fasa wani abun fashewa.
Lamarin da ya janyo wasu sassan cocin barnacewa da lalacewa sakamakon fashewar abun fashewar da aka sanya, hakan kuwa ya janyo fargaba a zukatan jama’an yankin.
Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin, sai dai wasu uku da ‘yan banga suka kama bisa zarginsu da hannu kan lamarin sun mika su ga ‘yan sanda ya zuwa yanzu.
Jami’an tsaron sun mamaye wurin tare da kewashi, tun bayan faruwar lamarin.