An Cafke Mutumin Da Ake Zargi Da Sayar Da ‘Yarsa A Adamawa

Yarsa

Rundunar ‘yansanda ta jihar Adamawa, ta damke wani mutum da ya fito daga karamar hukumar Mayo-Belwa bisa zargin sayar da ‘yarsa.

Mutumin wanda aka sakaya sunansa an gurfanar da shi a gaban kuliya, bisa zargin da ake yi masa a kan batan ‘yarsa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje, ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Alhamis.

Nguroje ya ce, wanda ake zargin ya fada wa ‘yansanda cewa, ya tawo da ‘yar ta sa kasuwa ne don ya sayi kayan abinci ta kai masa gida.

Kamar yadda ya ce ya sayi kayan abinci, a kasuwa ya ba ‘yar ta kai gida, amma sai ba  a ga yarinyar ba.

Haka kuma tun da suka rabu bai sake ganin yarinyar ba, sai wani gari, mai suna Mayo-Belwa, kamar yadda ya shaidda wa ‘yansanda.

jami’in hulda da jama’a na rundunar ;yansanda ya ce, yanzu haka ‘yansandan na ci gaba da gudanar da bincike, wanda da zarar an gama binciken za a gabatar da  wanda ake zargin a gaban kotu.

Sahabi Joda, wanda ke zaune a Mayo-Belwa, ya gayawa ‘yansanda cewa wannan abin ya faru ne ranar Talatar da ta gabata.

Majiyar labarinmu ta tabbatar da cewa, makocin wanda ake zargin mai suna Joda, ya tabbatar da cewa, ya ga yarinyar tare da  nakocin nasa, wanda kuma tun daga wannan lokacin ne bai sake ganinta ba.

 

Exit mobile version