An Cafke Uwa Da Laifin Kulle Danta Tsawon Shekaru 28

Kurkuku

An kama wata uwa a kasar Sweden bisa zargin kulle danta a cikin gidansu na tsawon shekaru 28, kuma ta bar shi da rashin abinci mai gina jiki wanda ya yi sanadiyyar hana hakorinsa fitowa, in ji ’yan sanda da kafofin yada labarai a ranar Talata.

“Ana zargin mahaifiyar ne da hana ‘yanci kai ba bisa ka’ida ba da kuma haifar da lahani a jikin dan Adam,” in ji kakakin’ yan sanda na Stockholm Ola Osterling a gaban AFP.

Ya ce, mutumin ya kasance an kulle shi na tsawon lokaci a cikin gidan da ke kudancin birnin Haninge na Stockholm, amma ba zai ce komai ba game da rahotannin da jaridar Edpressen da Aftonbladet suka bayar cewa an tsare shi na tsawon shekaru 28.

Rahotannin sun ce mahaifiyar ta cire danta daga makaranta tun yana shekara 12 kuma ta garkame shi a cikin gidan tun daga lokacin. Wani dan uwan da ba a bayyana sunansa ba ne ya sami mutumin mai shekaru 41 yanzu a ranar Lahadi bayan an kai mahaifiyarsa, ‘yar shekaru 70, zuwa asibiti, Edpressen ta ruwaito.

Rahotannin sun ce, mutumin ya kamu da ciwo a kafafunsa, da kyar ya ke iya tafiya, ba shi da hakora kuma ba ya iya magana. Osterling ba zai ce komai game da wadannan bayanai ba, yana mai cewa, “Mutumin yana asibiti. Raunin da ya ji ba na barazanar rai bane.”

Mahaifiyar ta musanta aikata laifin, in ji hukumar shigar da kara ta Sweden.

Likitocin da asibitin suka sanar da ‘yan sanda game da lamarin. ‘yar uwar mahaifiyar da ba a san ta ba wanda ta sami mutumin, ta ce, gidan kamar ba a tsaftace shi cikin shekaru ba. Ya ce, “Akwai fitsari, da datti da kuma kura. Ya ji warin rubewar wani abu. Dole ne ta ratsa ta cikin tarkacen shara don wucewa ta farfajiyoyin, saboda ba bu wanda ya tsabtace gidan tsawon shekaru.”

Ta kara da cewa, “Ina cikin matukar damuwa, amma a lokaci guda na samu salama. Na kasance ina jiran wannan rana tsawon shekaru 20 saboda na gano cewa tana sarrafa rayuwar danta gaba daya, amma ban taba tunanin abin ya kai girman hakan ba. Ina godiya kawai da ya samu taimako kuma zai rayu.”

Exit mobile version