Daga Rabiu Ali Indabawa,
Wani da ake zargi da safarar miyagun Kwayoyi da Hukumar hana Sha da fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, an fitar da hodar iblis 86 daga cikin kayansa, a cewar hukumar. Mai magana da yawun NDLEA, Jonah Achema, ya ce wanda ake zargin, Oluchukwu Onu Juma’a, mai shekaru 39, an kama shi ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kamfanin jirgin saman Ethiopian Airline ET910 zai tashi a Abuja zuwa Addis Ababa daga can zuwa New Delhi.
Achema, a cikin wata sanarwa a jiya, ya ce, Onu, dan asalin kauyen Umuaku-Isiochi a Jihar Abia, an tare shi ne a lokacin da aka bincike a kofar shiga jirgi kuma aka tura shi don yin binciken inda ya tabbatar da cewa ya aikata hakan. Mataimakin Kwamandan masu safarar kwayoyi ya ce wanda ake zargin ya fitar da wasu kayan hodar iblis 86 wadanda suka tabbatar da cewa hodar ce bayan gwajin kwayoyi kuma an auna inda nauyinta ya kai kilogram 1.527.
Sanarwar ta ce: “Onu, dillalin da ke zaune a Legas inda ake sayar da kayayyakin gini, an yi masa alkawarin Naira miliyan 1.5 a kan nasarar isar da shi ga wanda zai karba a New Delhi, Indiya. “Ina sayar da kayayyakin gini a Legas. Na yanke shawarar yin wannan tafiya ne don in sami damar tallafawa kasuwancina. Na yi asarar kudade masu yawa a yayin Korona, don haka ina bukatar wata hanyar samun kudin shiga ‘, in ji Onu.
“Onu, wanda ya kammala karatun firamare, ya yi aure a shekarar da ta gabata kuma matarsa na jiran tsammani. “A cewar Kabir Sani Tsakuwa, Kwamandan NDLEA a Filin jirgin saman Abuja, ana kan gudanar da bincike domin tarwatsa cibiyar safarar miyagun kwayoyi ta Onu. “Wannan kamun da ake a wannan lokacin shi ne mafi muni saboda kusan yawan adadin kayan ana hadiye wa ne ko kuma su yi allurarsa.