Mahdi M Muhammad" />

An Cafke Wani Matashi Akan Satar Matar Wansa A Zariya

’Yan Fashi

An cafke wani saurayi tare da abokansa kan sace matar babban yayansa a Dutsen Abba da ke karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.

Rahoto ya tattaro cewa, ’yan bindigar sun kai hari a kauyen Madaka da ke Unguwar Dutsen Abba a ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da Samira Sani da kuma wata matar gida.

Mijin Samira wanda shi ne Kansilan Dutsen Abba, Abdulaziz Sani, ya bayyana cewa, ’yan banga sun kame kanen nasa ne tare da abokansa biyu, bisa zargin leken asirin wadanda aka sace tare da ba da bayanai ga masu satar mutane a yankin.

Rahoto ya ci gaba da cewa, ’yan bindigar sun kuma kai hari a kauyen Unguwar Hazo da ke Dutsen Abba inda suka kashe wasu matasa biyu, Musa Isa, dan shakaru 28, da Yusuf Sulaiman, dan shekaru 30.

‘Yan bindigar sun kuma harbi wata mata ’yar shekara 64 da kuma wata mai shekaru 50, amma duk suna karbar magani a asibiti.

Sun kuma kwace baburan Boder guda hudu a cikin gidan dan majalisar.

Sai dai kungiyar ‘yan banga ta jihar Kaduna sun tare ‘yan bindigar a Unguwar Mai Tirmi da ke karamar hukumar Igabi inda suka ceto matan da aka sace tare da kwato baburan da suka wawure daga hannun mutane.

Exit mobile version