Wani wanda ake zargi da laifin damfara da aka bayyana da suna, Kelbin Odion, wanda ya kware wajen silale katin cirar kudi ‘ATM’ daga aljihun mutane wadanda ba su sani ba, inda yake amfani da katin da ya sata wajen cirar kudi daga asusun bankin mutane, ya ce, ya fara aikata wannan laifin ne a shekarar da ta gabata a watan Disamba, inda ya tara kusan Naira 200,000 a matsayin nasa gudummawar domin binne mahaifinsa a jihar Edo.
Kelbin wanda aka ce an kama shi a Ijebu Ode tare da kati 17 na ATM tare da wasu mutane 58 da ake zargi da aikata laifi a ranar Laraba a ofishin ‘yan sanda na jihar Ogun, Eleweran, Abeokuta da aikata laifuka daban-daban da suka hada da kungiyar asiri, satar mutane, fashi da makami, yunkurin kisan kai da sauransu.
Kelbin wanda ya shaida wa wakilinmu cewa, a da yana sayar da takalmi ne a Mandillas, Jihar Legas, sai daga baya ya yanke shawarar yaudarar mutane ta hanyar amfani da katin ATM dinsu da ya sace, duk a kokarin tara N200,000 a matsayin gudummawarsa don binne mahaifinsa.
Ya ci gaba da cewa, ya yi nadama kwarai da gaske da ya shiga harkar yankar aljihun mutane da nufin neman kudinsu, yana mai bayanin cewa, da ya son cewa za a cafke shi da wuri da bai yi hakan ba. Ya samu Naira kusan 95,000 a harkar kafin lokacin da ‘yan sanda suka kama shi.
Da yake magana a kan wanda ake zargi da damfarar, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Edward Awolowo Ajogun, ya ce, wanda ake zargin ya yi nasarar sauya katin ATM na mutane biyu sannan ya fidda kudi Naira 40,000 da Naira 55,000 daga asusun wadanda abin ya shafa.
Ajogun ya ce, “Wanda ake zargin duk da haka bai yi sa’a ba lokacin da daya daga cikin wadanda ya sace katin su ya ganshi a wani banki yana kokarin ciran kudi da katin wani mutum, a inda ya mutumin ya yi kururuwa kuma nan take aka kama shi.”
Shugaban ‘yan sanda ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin ne tare da katin ATM daban-daban har 17. Kwamishinan, ya gargadi masu aikata laifi da su kaura daga jihar, yana mai cewa, ‘yan sanda za su ci gaba da tabbatar da cewa babu wani yanki na jihar da zai dace da masu aikata laifi.
Wadanda aka gurfanar din sun hada da wasu mutane 25 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da aka kama a lokacin wani biki a Abeokuta. Ajogun, ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne tare da wasu likitocin magani uku da suka gudanar da farawar.
Baya ga ‘yan kungiyar asirin, an gurfanar da wasu mutane 34 da ake zargi da aikata laifuka kamar fyade, satar mutane, kisan kai, fashi da makami da zamba.
Ajogun ya bayyana cewa, an cafke ‘yan kungiyar asirin ne bayan rahoton sirri da aka samu da ke nuna cewa, wasu mambobin kungiyar suna shirin tayar da rikici a kan jama’a bayan sun gudanar da bikin fara sabuwar kungiyar a yankin Ita-Oshin da ke Abeokuta.
Ya kara da cewa, ‘yan sanda sun kwato gatari na yaki, adduna da tabar wi-wi daga wadanda ake zargin, da kuma kayan kungiyar su. Shugaban ‘yan sandan ya kuma gabatar da wadanda ake zargi da kisan mutum uku, Ugo Obi, Chinozo Jude da Chibuike Samson bisa zargin yiwa wani saurayi mai shekaru 23, Samuel Ajibade dukan tsiya har lahira kan zargin satar waya.
A cewar kwamishinan, mutanen ukun sun bugi mamacin ne tare da lakada masa duka har lahira kan zargin satar wayoyin hannu biyu da daya daga cikinsu ya yi.
‘Yan sanda sun kuma gabatar da wani mutum mai suna Tunde Bello, wani direban tasi da ya yi awon gaba da wata yarinya ‘yar shekara 29 da haihuwa tare da yi ma ta fyade.
Ajogun ya ce, wanda ake zargin ya sace yarinyar ne a lokacin da take kan hanyarta ta zuwa aiki a watan Satumbar, 2020 kuma sai da ya karbi Naira 140,000 kafin ya sake ta.