Gwamnatin jihar Katsina ta ce an samu nasarar ceto yaran makarantar sakandaren Kankara su 340 a yau Alhamis da daddare. Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Mustapha Inuwa ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce a yanzu haka ana hanyar kai yaran birnin Katsina daga garin Tsafe na jihar Zamfara da ke makwabtaka da jihar.
Ya kara da cewa a daren yau za a tarbe su a Katsina bisa kulawar jami’an tsaro, sannan a gobe Juma’a Shugaba Buhari zai gana da su a birnin Katsina. Nisan tafiya daga garin Tsafe na Zamfara zuwa birnin Katsina ya kai kilomita 213, tafiyar da za ta dauki sa’a kusan uku saboda rashin kyan hanya.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu yan bindiga suka dirar wa makarantar kimiyya ta kwana ta maza da ke garin Kankara inda suka yi awon gaba da yara kusan 400. Kwana hudu bayan haka sai shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da sako yana ikirarin sace yaran. Ko a ranar Alhamis da rana ma kungiyar Boko Haram din ta fitar da wani bidiyon daliban.