An Ceto Mutane 18 Yayin Da ‘Yansanda Suka Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Katsina
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Ceto Mutane 18 Yayin Da ‘Yansanda Suka Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Katsina

bySadiq
3 years ago
'Yansanda

Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta ce ta dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwar Gatakawa da ke karamar hukumar Kankara ta jihar.

Gambo Isah, kakakin rundunar, ya ce jami’ansu sun kuma ceto mutane 18 da aka sace.

  • 2023: Kuri’a Miliyan 95 Ce Za Ta Bayyana Wanda Zai Gaji Buhari – INEC
  • Gwamnatin Kano Ta Yi Allah-Wadai Da Hare-Hare Da Kwacen Wayoyi Da Magoya Bayan NNPP Ke Yi

Isah ya bayyana cewa, a ranar 12 ga watan Oktoba, da misalin karfe 1 na dare, rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya inda wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai farmaki kauyen, inda suka rika harbe-harbe.

Isah ya ce “Da samun rahoton, DPO na Kankara ya jagoranci runduna ta musamman zuwa yankin inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.

“Rundunar ta yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar da ake zargi da aikata munanan ayyuka tare da kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su.”

Sai dai ya kara da cewa an kashe mutane biyu a yayin harin.

“A yayin da ake duba wurin, an gano babura biyar da shanu biyu. Abin bakin ciki shi ne, mutanen kauye biyu sun mutu sannan daya ya ji rauni a hannu.

“Ana fargabar cewa an kashe da dama da ake zargin ‘yan fashi ne ko kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga. Ana ci gaba da gudanar da bincike.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Manyan Labarai

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Next Post
Za A Yi Amfani Da Na’urorin Noma Na Zamani Wajen Gudanar Da Aikin Cirar Akasarin Audugar Da Aka Noma A Xinjiang

Za A Yi Amfani Da Na’urorin Noma Na Zamani Wajen Gudanar Da Aikin Cirar Akasarin Audugar Da Aka Noma A Xinjiang

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version