Connect with us

MANYAN LABARAI

An Ceto Mutum Shida Daga Rushasshen Gini A Kano

Published

on

Ma’aikatan kwana-kwana sun samu nasarar ceto rayukan wasu mutum shida, da gini ya ruguzu a kansu a yammacin jiya Laraba a Unguwar Gwammaja dake karamar hukumar Dala a Jihar Kanon Dabo, cikin wadanda aka ceto din harda yaro dan shekaru 10 da haihuwa.

Ma’aikatan kwana-kwana sun samu kiran neman ceto ne da misalin karfe 8:14 na daren jiya daga wani mazaunin unguwar mai suna Kabiru Yusuf, inda ba su yi wata-wata ba wajen tura jami’ansu da kayan aikin ceto ciki harda mota, jami’an sun isa wajen da abun ya faru da misalin karfe 8:30 na daren.

Mutum biyu daga cikin wadanda aka ceto din sun rasu a kan hanyar kai su asibitin Malam Aminu Kano, sauran mutum hudun kuwa suna nan rai a hannun Allah a asibitin.

Wadanda aka ceto din sune, Muhammad Malami dan shekaru 10, Abba Malami, shekaru 12, Salim Malami, shekaru 14, Asmau Malami, shekaru 16, Maryam Malami, shekaru 18, sai kuma Zainab Malami mai shekaru 50.

Har yanzu dai hukumomi suna binciken musabbabin wannan al’ammarin ma rushewar gini, wanda ana kyautata zaton ruwan sama mai karfi da yake sauka ne ya jawo shi.

 




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: