Yusuf Shuaibu" />

An Ceto Tsohuwa Mai Shekaru 80 Daga Hannun Masu Garkuwa

Rundunar ‘yan sanda Jihar Bayelsa ta samu nasarar ceto wata tsahuwa mahaifiyar shugaban karamar hukumar Yenagoa mai suna Madam Beauty Nimizuoa, wacce aka yi garkuwa da ita tun kwanaki 21 da suka gabata.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, an yi garkuwa da tsohuwar ne tun a ranar 5 ga watan Maris, a gidanta da ke yankin Agudama-Epetiama cikin babban birnin jihar. Masu garkuwan sun bukaci a ba su kudin fansa na naira miliyan 70.

Majiyarmu ta ruwaito mana cewa, a ranar Asabar ce aka samu nasarar ceto tsuhuwar daga hannun masu garkuwan bayan bibiyar wayarsu da musayar harbin bindiga a maboyarsu da ke yankunan Ughelli cikin garin Warri da Ezetu a Jihar Delta da kuma Jihar Bayelsa.

Tawagar ‘yan sanda ta musamman karkashin jagorancin DSP Chris Nwaogbo sun sami nasarar damke mutum daya wanda ake zargin yana daya daga cikin masu garkuwa da mutane a Jihar Delta. Sauran masu garkuwan sun gudu da raunikan harbi lokacin da suka fafata a tsakaninsu da ‘yan sanda.

An bayyana cewa, mutum dayan da aka kama daga cikin tawagar masu garkuwa da mutane mai suna John, ana zargin ya kammala karatunsa ne a Jihar Abiya. A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda Jihar Bayelsa ta bayyana saukar sabon kwamishinan ‘yan sanda jihar, Nkereuwem Akpan. Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nkereuwem Akpan ya maye gurfin tsohun kwamishinan jihar, CP Uche Anozia.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da wannan rahoto. Ya bayyana cewa, sabon kwamishinan  ‘yan sandar jihar ya fara gudanar da aiki ne tun a ranar 26 ga watan Maris ta shekarar 2020. Kafin a ba shi wannan mukami, ya rike kwamishinan ‘yan sanda ta Jihar Kuros Ribas. Shi ne jami’an dan sanda  da ke jagorantar gudanar da ayyuka a mabambamtar rundunar ‘yan sanda na jihoji daban-daban.

 

Exit mobile version