Hukumar dake kula da gudanar da gasar Firimiyar Nijeriya ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars naira miliyan tara, bayan da ta sameta da laifin karya dokar gasar haka kuma hukumar ta kwashe maki uku daga wanda Pillars take da shi, duk dai a cikin hukuncin da aka yanke mata.
Wannan hukuncin ya biyo bayan da magoya bayan Kano Pillars suka ragargaji motar Katsina United, bayan wasan hamayya da Katsina United karawar mako na 22 ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha da ke Jihar Kano. Wannan kuma shi ne karon farko da Kano Pillars ta yi fafatawa a gida, tun bayan kakar wasa biyu da take buga wasanninta a Jihar Kaduna, bayan da filin wasa na Sani Abacha bai cika ka’idar karbar bakuncin wasannin Firimiyar Nijeriya ba.
Kawo yanzu Pillars za ta biya tarar Naira miliyan tara, an kuma kwashe mata maki uku, za ta koma buga wasannin da suka rage mata a filin wasa na MKO Abiola da ke Babban Birnin Tarayya Abuja. Haka kuma za a sake cire mata maki uku nan gaba idan an sake samun kungiyar da tayar da hatsaniya kuma cikin hukuncin an umarci Kano Pillars da ta gyara motar Katsina United da aka lalata a lokacin da za ta karkare wasanninta a Abuja.
Da wannan maki ukun da aka kwashe, Kano Pillars ta yi kasan teburi zuwa ta 16 da tazarar maki biyu tsakaninta da ‘yan karshen teburi sannan Pillars din za ta buga wasan mako na biyun da ba a karasa shi ba da Katsina United a Abuja ranar Litinin mai din nan.