Abba Ibrahim Wada" />

An Ci Tarar Liverpool Kan Amfani Da Dan Wasan Da Bai Dace Ba

An ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool fan dubu dari biyu (200,000), bayan da aka sameta da laifin saka dan wasan da bai dace ba a gasar cin kofin Caraboa Cup a makon jiya a wasan da ta yi da MK Dons.

Dan kasar Spaniya, Pedro Chiribella, mai shekara 22 ya shiga karawar da Liverpool ta yi nasara a kan MK Dons da ci 2-0, inda ya sauyi dan kwallo, amma bai da takardar tantacewa ta kasa da kasa kamar yadda rahoto ya tabbatar.

Hukumar EPL ta ce Liverpool za ta fara biyan fan 100,000 daga baya ta cika sauran a kakar Caraboa ta badi sannan kuma ta gargadi kungiyar, akan cewa kada ta kuskura ta sake aikata irin wannan laifi anan gaba.

Chiribella na bukatar takardar tantancewa daga hukumar kwallon kafa, bayan da ya buga wasannin aro a wata kungiyar Spaniya, Edtremadura a bara sai dai Liverpool batayi kokarin samu wanann izini ba.

Idan kuma Liverpool ta sake aikata irin wannan laifin za ta biya sauran tarar fan 100,000 da dakatarwa, da zarar ta saka wani dan wasan da bai dace ba kafin kammala wasannin bana kamar yadda hukumar ta bayyana.

An ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Sunderland a shekarar 2014 a gasar firimiya da kuma gasar League Cup, bayan da ta saka dan kwallon da bai dace ba a wasannin firimiya hudu da kuma League Cup din.

Exit mobile version