Daidai lokacin da ake cika watanni 6 da bullar cutar coronabirus ko kuma COBID-19 a duniya, hukumar lafiya ta WHO ta yi gargadin cewa ko kadan ba a wuce annobar cutar coronabirus ba, domin kuwa a yanzu haka somin tabi aka fara gani na bannar da cutar za ta yiwa duniya.
Cikin bayanan da WHO ta fitar jiya, bayan cika watanni 6 da bullar cutar wadda a karon farko ta bayyana a yankin Wuhan na tsakiyar China, shugaban hukumar Tedros Adhanom, ya ce duk da matakan da kasashen duniya ke dauka na yaki da cutar a kowacce rana adadin masu kamuwa da ma wadanda ke mutuwa na sake karuwa, wanda ke nuna bannar da cutar za ta tafkawa duniya gabanin zuwa karshenta.
Tedros Adhanom a jawabin nasa, ya ce watanni 6 da suka gabata, babu wanda ya yi tunanin annobar cutar ta coronabirus da ta faro daga China za ta jefa duniya a halin tsaka mai wuya.
Acewar hukumar ta WHO yaki da coronabirus na bukatar hakuri tare da aiki tare, domin kuwa sai an hada hannu ne za a iya yaki da ita, yana mai cewa sai a nan gaba ne cutar za ta kai ganiyarta.
Bugu da kari, Majalisar Dinkin Duniya ta ce annobar coronabirus ta jefa akalla yara sama da miliyan 100 a yankin Kudancin Asia cikin talauci sakamakon yadda cutar ta shafi tattalin arzikin yankin. Daraktan Hukumar da ke kula da Yankin Jean Gough ya ce matsalar ta shafi yin rigakafin cuttutuka da samar da abinci mai gina jiki da kayan more rayuwa, inda ya bukaci daukar matakan gaggawa domin rage radadin matsalar.
Yankin kudancin Asia na dauke da yara miliyan 600 da suka fito daga kasashen India da Pakistan da Afghanistan da Nepal da Bangladesh da Sri Lanka da Maldibes da Bhutan, kuma miliyan 240 daga cikin su na fama da tsananin talauci.
A wani rahoton kuma, karuwar adadin masu dauke da cutar coronabirus a sassan duniya ta sa hukumomi a wasu kasashe, ciki har da India da Amurka, sun sake kakaba dokokin kulle, yayin da shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce har yanzu ba a dauki hanyar shawo kan cutar ba.
India ta ba da rahoton samun karin adadi mafi yawa na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jiya Litinin inda ta samu mutum 20,000, wanda ya haura sama da dubu mutum 100,000 da aka gani a cikin mako daya.
Kasar ita ke biye da Amurka, Brazil da kuma Rasha a adadin wadanda aka tabbatar sun harbu tun lokacin da annobar da ta faro daga China a karshen shekarar da ta gabata.
Sai dai wani bangare na jihar Assam da ke Indiar ya sake kakaba dokar kulle har zuwa 12 ga watan Yuli, yayin da jihar West Bengal ta kara tsawaita dokokin kullenta har zuwa karshen watan na Yuli.
A Amurka kuwa, jihohin Tedas, Florida, Arizona da kuma California na daga cikin wadanda suka ga karin wadanda suka kamu da cutar.