An Cimma Nasarar Gudanar Da Taron Shawarwarin Ciniki Tsakanin Sin Da Nijeriya
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Cimma Nasarar Gudanar Da Taron Shawarwarin Ciniki Tsakanin Sin Da Nijeriya

byCMG Hausa
3 years ago
Nijeriya

A ranar 30 ga watan Agusta, an kira taron shawarwarin ciniki a tsakanin kasar Sin da Nijeriya ta kafar bidiyo a biranen Beijing, da Fujian na kasar Sin, da kuma wasu sassan Nijeriya.

An gudanar da taron ne bisa hadin gwiwar sashen hulda da bangarorin ketare na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, da gwamnatin lardin Fujian, da ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Nijeriya da kuma gwamnatin jihar Kano.

  • Ya Wajaba Amurka Ta Kaucewa Sake Maimaita Irin Kuskuren Da Ta Aikata Game Da Taiwan

Mataimakiyar shugaban sashen hulda da bangarorin ketare na kwamitin tsakiyar JKS Shen Beili, da sakataren Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya Iyiola Omisore sun halarci taron, tare da gabatar da jawabai.

Nijeriya

A jawabinta, Shen Beili ta ce, kasar Sin za ta karfafa mu’amalar dake tsakaninta da jam’iyyun siyasan Nijeriya, da kare dangantakar cude-ni-in-cude-ka a tsakanin kasashen duniya, da aiwatar da jadawalin raya kasa da kasa, da inganta shawarar “ziri daya da hanya daya”, da karfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka bisa yarjejeniyoyin da aka kulla a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC.

A nasu bangare kuma, Iyiola Omisore da wasu jami’an Nijeriya, sun yi bitar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da Nijeriya da dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, inda suka jaddada cewa, kasar Sin aminiyar Nijeriya ce, kuma ana fatan ci gaba da habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, musamman ma a fannonin ciniki da zuba jari, da gina ababen more rayuwa, da ayyukan gona da samar da abinci da sauransu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Ancelotti Ya Kafa Tarihi A Real Madrid

Ancelotti Ya Kafa Tarihi A Real Madrid

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version