Wata mata mai suna Selbi ‘yar shekaru 42 daga Chennai, Indiya ta ji cewa akwai wani abu ba daidai ba lokacin da ta farka, inda ta fara jin kan ta kamar ba shi ba. Bugu da kari, wurin da take jin abin sai kaikayi yake kuma da alama wani abu na motsi. Nan take ta nufi asibitin Kwalejin Kiwon Lafiya ta Stanley don yin gwaje-gwaje. Yayin da daya daga cikin likitocin dakin gaggawa suka yi aikin gwajin, sun ga komai ya yi daidai, inda daga baya ya ga kafafun kwaro. Ba tare da sanin nau’in kwaron da ke ciki ba, sai likitan ya sanar da shugaban sashen kunne, Hanci, da Makogwaro na asibitin.
Kasancewar Shugaban sashen kwararre wajen cire kwari, tururuwa, da tsutsotsi daga kwanyar mutune, M.N. Shankar, ya san irin aikin. Ta amfani da sandar karfi da kuma karamin injin tsotse abu, ya yi ta fama da kwaron wajen fitowa har tsawon mintina 45. Hoton bidiyon abin da ya faru ya dauki sa’o’i da dama kafin aka samu nasarar cire kyankyaso. Ya fi inci tsayi, kuma abin mamaki shine, har yanzu yana raye. Nan da nan bayan cire shi, numfashin mai jinyar ya warware kuma ciwon kan ya fara raguwa.
Kodayake likitoci ba su san yadda kyankyason ya shiga jikin Selbi ba, sun yi kiyasin cewa yana iya kasancewa a cikin ta na kusan awanni 12.
Yana shiga ciki, sai kwaron ya fara hawa cikin kan matar ta ramin hancin ta. Wannan ya bar shi damar shiga cikin kasan kwanyar, wanda ke raba kwakwalwa da hanci.
Yayin da mara lafiyar mai shekaru 42 ta tsira daga mutuwa, Shankar ya yi gargadin cewa babu yadda za a yi a tabbatar da cewa wannan yanayin bai kara faru da wani ba.