Connect with us

WASANNI

An Cuci Griezman Da Oblak, Inji Kociyan Atletico Madrid

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Diego Semione ya bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta duniya bata yiwa ‘yan wasan kungiyarsa adalci ba kuma ta cucesu bayan bata zabe suba a cikin ‘yan wasan da zasu lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya da mai tsaron ragar da babu kamarsa.

Duka ‘yan wasan biyu, mai tsaron ragar kungiyar Oblak da kuma dan wasan gaba na kungiyar, Antonio Griezman sun taimakawa kungiyar ta Atletico tazama zakara a gasar Europa a kakar data gabata sannan Griezman ya lashe kofin duniya da kasar Faransa.

Amma babu daya daga cikinsu wanda Fifa ta saka sunansa acikin ‘yan wasa uku da aka ware domin zama gwarzon dan kwallon duniya da suka hada da Cristiano Ronaldo da Luca Modric da kuma dan wasan Liberpool Muhammad Salah.

Mai tsaron ragar kungiyar dai Oblak ya buga wasanni 49 a kakar wasan data gabata kuma wasanni 29 ba’a zura masa kwallo a raga ba yayinda ita kuwa Fifa tazabi mai tsaron ragar Faransa daya lashe kofin duniya, Lloris da mai tsaron ragar Real Madrid Thibaut Courtois sai kuma Kesper Scmeichel dan kasar Denmark dayake buga wasa a Leceister ta kasar Ingila.

“Duk duniya babu kamar Oblak a yanzu saboda yayi kokari yadda yakamata a kakar wasan data gabata ya taimaka mana mun lashe kofin Europa kuma munyi matsayi na biyu a gasar Laliga sannan ya buga wasanni da dama ba’a zura masa kwallo a raga ba” in ji Semione

Yaci gaba da cewa “Griezman kuma a kakar wasan data gabata babu wani dan wasa daya kaishi kokari shima ya lashe kofin Europa damu sannan kuma yaje ya lashe kofin duniya kofin da babu kamarsa a duniya”

Mai tsaron ragar daya lashe kyautar mai tsaron ragar da babu kamarsa dai a kakar data gabata shine tsohon mai tsaron ragar Jubentus, Buffon, wanda yanzu yake buga wasa a PSG ta kasar Faransa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: