Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bayar da sanarwar cewa tad age babban zaben shugaban kungiyar wanda aka tsara za’ayi a yau sakamakon dalilan cutar Korona da kuma shawarar da hukumomin kasar suka bayar.
Da farko dai an tsara cewa za’a gudanar da zaben ne a ranar 19 ga watan Janairu domin zabeb shugaban kungiyar saboda a halin yanzu kungiyar tana hannun rikon kwarya sai dai dalilai sun sanya an sake dage zaben.
Manyan ‘yan takarkaru dai da dama sun shirya fafatawa a zaben wanda yake cike da kalubale musamman ga wanda ya samu nasara domin akwai matsaloli jingim a kungiyar wadanda suke bukatar kallo na gaggawa.
Tsohon shugaban kungiyar, Joan Laporta ne a kan gaba tsakanin ‘yan takarar dake neman darewa shugabancin kungiyar bayan rage ‘yan takarar zuwa 4 daga 9 da akayi a kwanakin baya saboda magance sabon rikici bayan zabe.
Mai bi masa kuwa shine Bictor Font wanda yake da goyon bayan mutane dubu 4 da dari 710, tsohon jami’in hukumar gudanarwar Barcelona Toni Freida ya samu sa hannn mutane dubu 2 da dari 821, sai kuma tsohon mataimakin shugaban kungiyar Emili Rousaud da ya samu dubu 2 da dari 510.
Da farko dai babu sunan Laporta a cikin jerin ‘yan wadanda ake saran zasu fafata a babban zaben da za’ayi a wannan kakar sai dai tuni hankali ya koma kansa inda ake ganin zai iya sake komawa shugabancin kungiyar a karo na biyu.
Duk da cewa har yanzu babu wanda zai fayyace irin manufofin Laporta musamman dan gane da makomar dan wasan kungiyar kuma kaftin, Leonel Messi da kuma halin da kungiyar ta shiga na rashin kudi sakamakon annobar cutar Korona.
Har yanzu dai ba a sake bayyana ranar da za’ayi wannan zabe ba amma wasu rahotanni sun tabbatar da cewa a cikin watan Fabrairu mai zuwa za a yi zaben wanda shine karo na farko tun bayan sauka daga mukamin shugabancin kungiyar Jose Maria Bartemeu ya yi.