An Dage Raba Jadawalin Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika

Kofin Nahiyar Afrika

Hukumar kula da wasannin cin kofin nahiyar Afrika ta CAF, ta dage bikin fitar da jadawalin gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka tsara a birnin Yaounden kasar Kamaru ranar 25 ga watan Yuni.

Hukumar kwallon kafar Afirka ta CAF ce ta sanar da hakan a ranar Lahadi inda tace wasu dalilai ne suka sanya bata samu damar fitar da jadawalin ba amma kuma nan gaba kadan zasu bayyana lokacin da zasu fitar da jadawalin,

Hukumar ta ce ta ci karo da cikas wajen tsare-tsare da suka shafi hana yada cutar korona, amma nan gaba za ta sanar da sabuwar ranar da za a yi bikin wanda ake saran zai samu halartar shugabannin hukumomin kwallom kafa na  kasashe daban-daban.

A cikin watan nan kasashen Saliyo da Benin suka buga kwantan wasa kuma na karshe domin tantance kasashe 24 da za su fafata a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Kamaru za ta karbi bakunci cikin watan Janairu.

Tun a shekarar bara ya kamata a buga gasar, amma cutar korona ta haddasa da aka kawo wasannin zuwa shekarar 2021 sannan a watan jiya CAF ta dakatar da wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da aka tsara fara yi a farkon watan Yuni, domin gudun yada cutar korona.

Yanzu an tsayar da cikin watan Satumba, domin buga wasannin neman shiga gasar kofin duniya ta Katar 2022 da shiyyar Afirka za ta barje gumu domin fitar da kasashen da zasu wakilci yankin.

Exit mobile version