Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Shugaban Karamar Hukumar Kunchi Alhaji Aminu Idi Shuwaki ya bayyana cewa batun fashin zuwa aiki a karamar Hukumar Kunchi daga wannan rana ya zama tarihi, domin bazan dagawa kowa kafa ba, duk wanda ya zabi fashin zuwa aiki, ko shakka babu zan sa kafar wando daya dashi. Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Labara jim kadan da rantsar da kansilolin goma na karamar Hukumar ta Kunchi wanda aka gudanar a sakatariyar karamar Hukumar ta Kunchi.
Alhaji Aminu Idi Shuwaki ya ci gaba da cewa “ina son tabbatarwa da kowa da kowa tun daga kan shugaban ma’aikata har zuwa kan masinja ba wanda zai ci gaba da fashin zuwa aiki na zuba masa ido, daganan har gaban Gwamnan Jihar Kano, sai na tabbatar da ganin an hukunta duk wani mai kunnen kashi kan aikin da aka damka amanarsa a hannunsa. Saboda haka ina kira da babbar murya ba muda karamar Hukumar data wuce Kunchi, don haka dole mu zage damtse domin ciyar da yankin da muke alfahari dashi.
Da ya waiwayi bangaren ‘yan siyasa, Alhaji Aminu Shuwaki ya tabbatarwa da al’ummar Kunchi cewa shi bai yarda siyasara jagaliyanci ba, ma’ana bai yiwuwa kazo ka yaba masa, kuma ka koma gefe kana zagin wani dan siyasa, ko da kuwa ba jam’iyyar mu guda dashi ba, wanda duk ya aikata haka, ya sani har kofar gida zan aiki jami’an tsaro a damke shi. Mu siyasarmu na da kyakkyawar alkibla, alkiblar mu itace gaskiya da kishin kasa gami da al’ummar mu baki daya.
Da yake jawabin ga kansilolin da aka rantsar a wannan rana Alhaji Aminu Idi Shuwaki ya bukace su da su hada kai domin yin aiki tare, kasancewarmu ‘ya’yan wannan karamar Hukuma, wadda bamu da wani wuri da ya wuce ta. Saboda haka sai ya tabbatar masu da cewa an daina gudanar da aiki daga wani wuri, a karamar hukuma kowa zai fito ayi aiki, kuma dukkan wasu kadarorin Gwamnati dole su dawo aiki cikin karamar hukumar Kunchi domin kadarar al’ummar kunchi ne. Akarshe shugaban ya yi addu’ar fatan Allah ya shigo cikin al’amarin wannan sabon shugabanci.
An gudanar da bikin rantsar da kansilion a gaban Hakimin Kunchi, manyan daraktocin mulki, shugabannin sassan mulkin karamar Hukuma, jami’in ‘yan sanda mai lura da karamar Hukumar Kunchi, shugabannin jam’iyyar APC da sauran manyan mutane ne suka halarcin bikin rantsuwar.