Connect with us

WASANNI

An Dakatar Da Douglas Costa Wasanni Hudu

Published

on

Hukumar kula da wasannin kasar Italiya, ta haramta wa dan wasan gaba na Jubentus, Douglas Costa buga wasanni 4, sakamakon laifin da ya aikata na tofawa dan wasan kungiyar Sassuolo Federico Di Francesco yawu a fuska a wasan da suka fafata a ranar Lahadi.

Costa ya tofawa Di Francesco yawun a fuskarsa ne, yayin da suke fafata wasan gasar Seria A a karshen makon da ya gabata a wasan da Jubentus din tasamu nasara da ci 2-1 ta hannun dan wasa Cristiano Ronaldo.

Bayan sanar da yanke hukuncin, mai horar da Jubentus Massimiliano Allegri ya ce kungiyar ba za ta daukaka karar neman sokewa ko rage tsaurin hukuncin da aka yanke kan dan wasan nata ba.

Sai dai duk da haka Douglas Costa na cikin tawagar Jubentus da za ta fafata da kungiyar Balencia a wasan da suka buga jiya Laraba a wasan farko da kungiyoyin  suka buga na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Koda ya ke Costa ya nemi afuwar, abokan wasansa da magoya baya a sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, sannan dan wasan ya ce mutane basu da masaniyar irin muna nan kalaman da Di Francisco ya furta masa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: