An Dakatar Da Jigilar Jirgin Kasa Saboda Barazanar ‘Yan Bindiga

Barazanar ‘Yan Bindiga ta sa hukumar jiragen kasa ta Nijeriya ta tsayar da jigilar jirgin kasa a yau, wannan matakin ya biyo bayan sanya nakiya da ‘yan bindigar suka yi a kan hanyar jirgin kasan, a tsakanin Kaduna da Abuja, wanda hakan ya yi sanadiyyar lallata layin dogon. Bayan sanya nakiya, ‘yan bindigar sun budewa jirgin wuta, a kokarinsu na tsayar jirgin.

A jiya Laraba ma sai da ‘yan bindigar suka sanyar nakiya a kan layin dogon, kuma nakiyar ta fashe, inda saura kadan jirgin ya tintsire, sannan suka bude wuta, da safiyar yau Alhamis ma sun kuma yadda suka da yammacin jiya Laraba, amma basu samu nasarar tsaida jirgin ba. An ce lamarin ya faru ne a kusa da garin Rijana da ke jihar Kaduna.

Hukumar NRC mai kula da jigilar jiragen ta tura sakonni ta manhajar da ake sayen tikitin jirgin kasan, inda ta bayyana cewa yau babu wata jigila da jirgin zai sake yi, har sai hukumomin sun shawo kan wasu matsaloli, duk da basu bayyana wasu matsaloli bane, amma hakan baya rasa na saba da barazanar ‘yan bindigar. Cikin wanda abin na yau Alhamis ya rutsa da su, hara Sanata Shehu Sani, inda ya bayyana a shafinsa na Facebook, cewar sun tsallake rijiya da baya, yayin da ‘yan bindiga suka farmaki jirgin kasa karo na biyu a cikin kwama daya.

Exit mobile version