Hukumar yaki da shan kwayoyin karin kuzari ta duniya ta haramta wa mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Ajax dan asalin kasar Kamaru Andre Onana daga buga wasanni na tsawon shekara guda bayan samun mai tsaron ragar da laifin shan kwayoyi masu kara kuzari.
Sai dai cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta Ajax tace gwaji ne ya gano tasirin kwayoyin karin kuzarin a jikin Onana wanda kuma hukumar kwallon kafa ta duniya ta haramta shan kwayoyi masu kara kuzari ga ‘yan wasa.
Sai dai tace daga bisani bincike ya nuna mai tsaron ragar tata, ya kyankyami maganin Furosemide mallakin matarsa ne a bisa kuskure, bayan fama da masassara a ranar 30 ga watan Oktoba, wanda ke cikin kwayoyin da aka haramtawa ‘yan wasa.
A kokarin ta na nemawa mai tsaron ragar tata sassauci, Ajax ta ce hatta hukumar UEFA na da tabbacin cewar Andre Onana bai kurbi maganin Furosemide da nufin ha’inci ba, saboda haka za ta kalubalanci hukuncin dakatar dashi daga buga wasanni na tsawon shekara guda ta hanyar daukaka kara a gaban kotun kula da harkokin wasanni ta duniya.
Tuchel Ya Karya Tarihin Mourinho A Chelsea
Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Thomas Tuchel ya kafa tarihin zama mai horar da kungiyar na farko cikin shekaru 16 da ya jagoranci wasanni 3 na farko bayan kama aiki ba tare da yayi rashin nasara ba.
Mai koyarwa Tuchel ya kafa tarihin ne bayan doke kungiyar Tottenham da ci1-0, yayin fafatawar da suka yi a gasar Premier ranar Alhamis kuma rabon da wani sabon koci ya samu irin wannan nasara a Chelsea tun cikin watan Agustan shekarar 2004, lokacin da Jose Mourinho ya karbi ragamar jagorancin kungiyar sannan yanzu haka Chelsea ce ta shida a gasar Premier da maki 36.
Bayan tashi daga wasan Tuchel ya jinjina wa ‘yan wasan kungiyar inda ya tabbatar musu da cewa idan suka ci gaba da dagewa suna mayar da hankali a ragowar wasannin da suke gabansu zasu bawa duniya mamaki.
“Tabbas akwai wahala a wasannin firimiya amma kuma yanayin yadda ‘yan wasa suke dagewa da kuma mayar da hankali wajen ganin muna samun nasara a kowanne wasa zai bayar da dama mu samu damar zuwa duk inda muke son zuwa” in ji Tuchel