An Dambace Tsakanin Boko Haram da ISWAP

ISWAP

Daga Muhammad Maitela,

Rahotanni sun bayyana cewa sabon sabani ya barke tsakanin magoya bayan kungiyar Boko Haram a karkashin Abubakar Shekau da bangaren ISWAP mai ikirarin fafitikar kafa daular musulunci a Afrika ta yamma, wanda dambacewar da ta jawo mutuwar yan ta’addan da dama.

Kafar yada labarai mai kwarmata ayyukan Alka’ida, mai suna Al Rabat ce ta bayyana cewa wannan rikicin ya kaure tsakanin kungiyoyin a kan iyakar kasashen Nijeriya da jamhuriyar Nijar.

Al Thabat, ta wallafa bayanin a shafinta a wata sanarwar da ta fitar ranar Jummu’a, inda ta ce, Jama’atu Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad, wadanda aka fi sani da Boko Haram, sun kashe yan kungiyar ‘Islamic State West Africa Province’ (ISWAP) a kauyen Sunawa wanda ke kan iyakar Nijeriya da Nijar.

A wani rahoton da gidan radiyon BBC ya wallafa ya bayyana cewa kungiyoyin sun dambace ne biyo bayan da ISWAP ta yi kutsen sace wasu matan da ke da alaka da kungiyar Boko Haram. Wanda Boko Haram ba ta yi wata-wata ba kawai ta kai wa ISWAP farmaki a sansaninta domin kwato matan.

A baya dai, kungiyar ISWAP bangare ce ta Boko Haram kafin daga baya ta balle daga karkashin ikon Shekau a 2016, wanda tun daga wannan lokaci aka rinka yi wa juna kallon hadarin kaji tare da fito-na-fito tsakanin su.

 

Exit mobile version