Umar A Hunkuyi" />

An Damke Hauwa Mai Rudar Mutane Da Kyawunta Ta Sace Su

A karshe dai an samu nasarar kama kyakkyawar matar nan mai suna Hauwa, wacce ta shahara wajen rudar mazaje ta kuma sace su ta hanyar jan ra’ayin su a bisa kyakkyawar kirar jiki da Allah Ya yi mata.

Ba boyayyen abu ne ba, yanda wasu masu matacciyar zuciya suka mayar da sace mutane domin karban kudin fansa a matsayin wata babbar sana’a ta su a cikin kasar nan. batun na satan mutane a sassan arewacin kasar nan kamar sauran sassan na kasar nan a kullum dada karuwa ya ke yi.
Kamar yanda rahoton ‘yan sanda ya nuna, an samu rahotannin satar mutane har 685 a farkon zangon shekarar 2019 kadai. Masu satar mutanan da kuma ‘yan bindiga a halin yanzun wuyar ta yi kwarin da hatta gwamnatocin Jihohi ma suna tattaunawa da su ne domin neman sulhu da su ko kuma su sako wasu da suka kama da ke a hannun su.
Misali kamar a Jihar Zamfara, bincike ya nuna yanda kusan kullum sai an sami rahoton sace wani ko wasu, a bisa yanda alamu suka nuna kamar gwamnatin Jihar ta gaza shawo kan wannan matsalar. Kuma a duk lokacin da aka sace wani ko wasu, sai iyalan wanda aka sace din sun biya makudan kudaden fansa kafin wadanda suka sace su din su sako su.
A bisa wata sanarwa da gwamnatin ta Jihar Zamfara ta fitar a watanni uku da suka gabata, an jimlace kudaden fansa da al’umma suka biya domin fanso ‘yan’uwan su da cewa ya kai naira Bilyan Uku a shekarar 2019 kadai.
Kamun da aka yi a kwanan nan, na wata mata mai suna Hauw Yunusa, wacce aka bayar da rahoton cewa shahararriya ce a wajen sace mutane a nahiyar ta arewacin Nijeriya, kamar yanda majiyar hukumomin tsaro suka tabbatar, kamun nata yana matukar taimaka wa wajen gano bakin zaren.
Matar mai suna HauwaYunus, ‘yar kabilar Fulani ce, tana kuma zaune ne a wani kauyan Jihar Nasarawa. Kamar yanda wani Jami’in tsaro mai suna Abdullahi Alhasan ya bayyana, “Hauwa asalin ta ta fito ne daga Jihar Jigawa, amma tana zaune ne a garin Masaka, da ke Jihar Nasarawa.
A cewar jami’in tsaron mai suna Alhassan, Hauwa kyakkywar mata ce, wacce ta taba yin aure har sau uku, amma auren nata yana mutuwa a sabili da rashin kyawun halin ta.
Daya daga cikin mazajen da suka auri Hauwa, a cewar Alhassan, ya bayyana cewa sau tari takan dawo gida ne a buge cikin maye. Duk kuma kokarin da aka yi domin ganin an gyara halin nata ya ci tura.
Hauwa a cewar jami’in tsaron, ta shahara wajen rudan mazaje su fada soyayya da ita, wanda a karshe za ta yi hadin baki a sace su, musamman manyan mutane, duk kuwa da cewa shekarunta 24 ne kacal a Duniya, amma lissafin ta’asar da ta aikata musamman wajen satar mutane ya wuce na mai shekarunta ya aikata su.
An bayar da rahoton fadin da ta yi da bakinta cewa, takan yi wa wasu daga cikin mutanan da ta sace fyade a bisa mummunar sha’awar da take da ita na saduwa da mazaje, musamman a bayan ta sha miyagun kwayoyin ta.
A wani lokaci an bayar da rahoton yanda Hauwa ta sami nasarar dukkanin samarinta daya bayan daya, ba kuma tare da sun san cewa ita ce ta kitsa satar na su ba, kowannen su kuma ya samu kansa ne da kyar a bayan da ya biya kudaden fansa.
A kwanan nan ne aka sami nasarar kama Hauwa a Abuja, inda ta bayar da shaida da bakinta kan yanda ta kitsa sace saurayinta na farko, wanda mai kudi ne yana kuma kulawa da ita sosai, amma da ta fahimci cewa yana da wasu ‘yan matan a bayan ita ne sai ta yanke shawarar karban makudan kudade a hannun sa, inda ta kitsa yanda aka yi aka sace shi.
Baya ga samarin nata, Hauwa kuma ta shaida wa masu yi mata tambayoyin yanda ta kitsa sace wata babbar kawarta mai suna Zainab, a lokacin da ta yi satan jin kawar nata tana waya inda take bayanin cewa za a turo mata kudi Naira 600,000. “Hakan ya sanya na kitsa sace ta domin na samu nawa rabon daga kudaden.”
“Takaici na shi ne, kawar nawa Zainab ta rasu a sakamakon azabar da ta sha a hannun wadanda suka sace ta din inda suka yi mata raunukan da suka yi sanadiyyar mutuwar ta.
A bayan mutuwar na Zainab ne, sai Hauwa ta ce ta shiga dakin kawar nata marigayiya Zainab, ta dauki katin ciran kudinta na ATM inda ta sace dukkanin kudadenta da suke a cikin asusun ajiyarta na banki. Ba ta kuma tsaya a nan ba, ta ma sace motar ta, ta sake wa motar fenti ta kuma siyar da motar, hatta dukkanin kayayyakin kawar nata masu amfani har da kayan sawanta duk ita ta kwashe ta kuma siyar da su.
Alhaki ya kama Hauwa a bayan wannan duka, inda Insifektan rundunar ‘yan sanda ta musamman, kuma mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari ya sami nasarar kama ta.
A yanzun haka tana hannun ‘yan sanda tana kuma bayar da bayanai a kan hanyar kawo karshen matsalar sace-sacen na mutane musamman a sassan arewacin kasar nan.

Exit mobile version