Umar Faruk" />

An Damke Wanda Ya Shirya Sace Matarsa Don Yin Kudi Da Ita

Kotu

Kotu ta tsare wani magidanci Usman Abdulkareem, bisa zarginsa da ake da sace matarsa. An tattaro cewa Usman ya hada kai da wasu mutane biyu da suka hada da abokinsa da wani boka don yin asiri da matar tasa. Ya kira matar tasa a waya sannan ya bukaci ta je ta same shi a wani gida wanda yake na bokan ne. Wata kotun Majistare da ke Ilorin a ranar Laraba ta bayar da umarnin tsare Usman Abdulkareem, wanda ake zargi da hada baki da wani mai maganin gargajiya da abokinsa don sace matarsa, a cibiyar gyara hali. ‘Yan sanda sun tuhumi Abdulkareem, wani mai maganin gargajiya, Babatunde Mohammed da wani abokinsa, Fatai Adisa da aikata laifuka biyu na hada baki tare da yin garkuwa da mutum, don aikata kisan kai, wanda hakan ya saba wa sashi na 97 da 274 na dokar kundin shari’a.

Alege ta dage sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu, domin ci gaba da zama, kamar yadda jaridar Banguard ta ruwaito.

Dan sanda mai shigar da kara, Saja Abubakar Issa, ya fadawa kotu cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa Abdulkareem shi ne wanda ya kira Mumeenat, matarsa, a wayar tarho sannan kuma ya nemi ta hadu da shi a gidan wanda ake kara na biyu da karfe 5:00 na yamma. Ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa Mohammed, boka ne, wanda ke yi wa mutane asirin kudi ta hanyar amfani da sassan jikin dan’adam. Issa ya roki kotu ta dage zaman don bai wa ‘yan sanda damar kammala bincikensu.

Sai dai kuma wadanda ake tuhumar, sun musanta aikata laifin.

Exit mobile version