Daga Bello Hamza,
Wata kotun yanki da ke unguwar Kasuwan Nama na garin Jos a jihar Filato ta yankewa wasu dalibai biyu hukuncin zama a gidan yari na tsawon wata 18 saboda kama su da laifin satar wasu na’urorin sadarwa wadda aka kiyasta kudin su ya kai Naira 41,000.
‘Yan sanda sun tuhumi Istifanus Amos da Jonathan Ayuba da laifin hada baki da sata, wasu alkalai biyu, Ghazali Adam da Hyacinth Dolnaan, suka yanke wa Amos da Ayuba hukuncin bayan da suka amsa aikata laifin su, Alkalan sun kuma basu zabin biyan tarar Naira 30,000 kowannen su.
Alakan sun kuma bayyana cewa, hukuncin zai zama darasi ga suran al’umma masu shirin fada wa cikin irin wannan halayyar na sata.
Gokwat ya kuma kara da cewa, wadanda aka yankewa hukuncin sun balla ofishin ne in suka sace kayan da aka kiyasta ya kai na Naira 41,000 .
Ya ce, laifin ya saba wa sashi na 59 da 334 da kuma 272 na dokokin Fanedt Kot na jihar Filato.