Abba Ibrahim Wada" />

An Dawo Zagaye Na Biyu Na Gasar Kofin Zakarun Turai

Champions League

A jiya aka ci gaba da wasannin zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun turai na Champions League wasan farko, inda Barcelona ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain a filin wasa na Nou Camp a jiya Talata.

Barcelona ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na bakwai, ita kuwa PSG ita ce ta ja ragamar rukuni na takwas a wasannin bana wanda aka fafata a shekarar data gabata a wasannin rukuni.
Barcelona wadda ta yi wasanni 22 a gasar La Liga mai maki 46, tana ta uku a kan teburi, PSG kuwa wadda ta buga karawa 25 a Ligue 1 tana ta biyu da makinta 54 sannan a tarihi Barcelona ta lashe Champions League biyar a tarihi, yayin da PSG ta kai wasan karshe a bara, inda Bayern Munich ta yi nasara a kanta da ci 1-0 sai dai kuma rabonda Barcelona ta dauki Champions League tun a kakar wasa ta 2010 zuwa 2011.

Karawa tsakanin Barcelona da PSG:
Wasa tsakanin kungiyoyin biyu kan ja hankalin masu bibiyar kwallon kafa, kuma a kakar wasa ta  2017 zuwa 2018 Barcelona ta sha kashi da ci 4-0 a gidan kungiyar PSG a Faransa sai dai a wasa na biyu ne da ake ganin Barcelona ta yi ban kwana da gasar, sai ta ci 6-1 ta kuma kai zagayen gaba.
Wasan yana daga cikin wanda za a dade ba a manta da shi ba a tarihi, koda yake Barcelona ce kan yi nasara a kan PSG idan suka hadu a gasar ta Zakarun Turai sai dai a kakar wasa ta shekarar 1994 zuwa 1995 PSG ce ta kai zagayen gaba a karawar da ta yi da Barcelona a zagayen 1994 zuwa 1995 Champions League kuarter Final
Barca 1-1 PSG / PSG 2-1
(PSG ta kai zagayen gaba da ci 3-2)
1996-97 UEFA Cup Winners’ Cup Final
Barca 1-0 PSG
2012-13 Champions League kuarter Final
PSG 2-2 Barca / Barca 1-1 PSG
(Barca ta kai zagayen gaba)
2014-15 Champions League Group F
PSG 3-2 Barca / Barca 3-1 PSG
(Barca da PSG suka kai karawar zagayen gaba)
2014-15 Champions League kuarter Final
PSG 1-3 Barca / Barca 2-0 PSG
(Barca ta kai karawar gaba da ci 5-1)
2016-17 Champions League zagaye na biyu
PSG 4-0 Barca / Barca 6-1 PSG
(Barca ta kai karawar zagaye gaba da ci 6-5)

‘Yan wasan da suka buga kungiyoyin biyu:
Rafinha
dan kwallon tawagar Brazil ya fara da koyon kwallo tun daga La Masia daga nan ya buga wa babbar kungiyar wasa ta 56 a tsakanin wasannin aro da ya yi a kungiyar Celta bigo da Inter Milan daga baya ya koma kungiyar PSG a farkon kakar bana.
Mauro Icardi
dan kwallon Argentina ya buga wa matasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona wasa na matakin ‘yan shekara 18 da 19 tsakanin shekarar 2008 zuwa 2011 daga nan ya koma kungiyar Sampdoria ta kasar Italiya.
Neymar
dan kwallon tawagar Brazil da zai buga wasan farko ba sakamakon jinya ya taka rawar gani a Barcelona inda ya yi wasa tare da Messi da kuma Luis Suarez kuma a lokacin duk kungiyar da suka kama sai ta ji a jikinta, ko dai Messi ko Neymar ko Suarez wani sai ya ci kwallo ko biyu daga ciki, sannan kungiyar ta buga wasa mai kayatarwa sai dai a shekarar 2017 Neymar ya koma PSG da buga wasa a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya.

Exit mobile version