An Fadakar Da Matasan Jihar Kebbi Kan Ilolin Shiga Bangar Siyasa

Daga Umar Faruk Birnin Kebbi,

Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA), reshen Jihar Kebbi, ta shawarci ‘yan siyasa da masu zabe da su bi ka’idojin dimokuradiyya da kuma tsarin zabe nagari a zaben qananan hukumomi da ke tafe a jihar.

Mista Joseph Yero-Machika, Daraktan NOA, ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, ya ce, an shirya jawo hankalin ‘yan siyasa da masu zabe don samun nasarar gudanar da zabe mai inganci a jihar.

Ya ce, taron manema labarai da ya kira don yi wa masu zabe da ‘yan siyasa bayanin shirin domin gudanar da zaben qananan hukumomi na gaskiya sahihi a fadin jihar.

“Aikinmu a NOA shi ne nasiha da wayar da kan jama’a game da manufofin gwamnati da shirye-shirye sannan mu dauki bayanan ko mai kyau ko mara kyau daga jama’a zuwa gwamnati.

“A zahiri, muna saukaka kwarara bayanai daga sama zuwa kasa, kuma daga sama zuwa sama, don haka zaben ba wani abu ne da ya kebanta da shi ba, don haka bukatar wannan shiri na tattara bayanai har zuwa fara yakin neman wayar da kanmu domin tabbatar da gaskiya da adalci ga zabe a jihar,” inji shi.

Daraktan ya shawarci matasa da su guji ’yan daba na siyasa, inda ya ce irin wannan hali na da illa kwarai ga nasarar zabe ba har ma da ci gaban al’umma.

“Ku tabbatar da cewa katin zabe na dindindin (PVCs) na hannunku kuma kada ku mika wa kowa saboda yin hakan tamkar mika makomarku da na ‘ya’yanku ga wanda baku sani ba.

“Wannan zaben da ya zo ranar 5 ga watan Fabrairun 2022, yana da matukar muhimmanci ta yadda ya taba tunanin al’ummar yankin, kasancewar sun rufe sosai ga ‘yan takarar jam’iyyu daban-daban na kusa da su,” in ji daraktan.

Exit mobile version