An Fara Bincike Kan Annobar Shan Kodin A Nijeriya

“Abun da maka gano yana da matukar tayar da hankali, mun gano tsananin girman annobar shan wannan maganain tarin a Nijeriya. Haka kuma mun gano girma da zurfin kungiyoyin ‘yan ta’aadan dake safarar wannan mugun maganin dake haukatar da matasa.” Inji Adejuwon Soyinka, Edita a sashin BBC Pidgin da ta gudanar da bincike.

Soyinka ya bayyana wa manema cewa, abubuwan da suka gano ya tayar da wasu muhimman tambayoyi.

“Daga cikin abin daya zaburar damu a kan wannan aikin shi ne irin yawan koken da muke samu daga iyaye na yadda yaransu musamman ‘yan makarantun sakandire ke fadawa kangin shaye shayen kodin.

“Gare mu wannan lamari ne mai tayar da hankali, nan take muka yi shawarar yin kyakyawar bincike saboda a tunaninmu lallai babban labari ne, amma a lokacin da muka fara shiga cikin labarin sai muka fahinci tsananin girma da fadin lamarin ya fi abin da muka yi tunani tun da farko.

“Sai muka gano cewa, lamarin ya wuce maganan ‘yan sakandire abin ya kai ga daliban jami’o’i domin kuwa rukunin matasa da dama duk sun fada, maganin tarin mai kodin ya zama ruwan dare musamman a wuraren shakatawa da wurin bikin murnar zagayowar ranar haihuwa da sauran matattaran matasa da ‘yan mata.

“Sannan abin da muka gano ya kara tayar mana da hankali, ba wai maganar shan kodin da ake yi kawai ya tayar mana da hankali kawai ba, har da yadda masu shan kodin din ke samun ainihin maganin tarin mai kodin masu yawa kuma a cikin sauki, wannan shi ne yafi tayar mana da hankali.

Soyinka, ya kara bayyana cewa, abin daya fi tayar da hankali shi ne yadda masu shaye shayen ke samun maganin tarin na kodin duk da cewa, magani ne da ake sanya wa ido a kai, ba a siyar wa mutum koda kwalba daya ba tare da an nuna takarda izini daga likita ba.

Kodin na daga cikin magungunar da ake sanya ido a kai, saboda haka ba a amfani da shi ba tare da umurni ko amincewar likita ba, ana ba mara lafiya ne domin magance tsananin radadadin zafi da kuma danne tari mai naci.

Haka kuma an tabbatar da cewar, kodin nada tsananin hatsari saboda yadda ake sha ba bisa ka’ida ba musamman tsakanin matasa da shahararrun masu mawaka. Bayanai daga litattafan likitoci ya nuna cewa, ana ba marasa lafiya kodin na ruwa ko na kwaya tare da taka tsantsan domin magance tsananin zafi da wani tari mai naci.

Amma masu shaye shaye na shan kodin ne saboda bugar dasu daya keyi da kuma sasu cikin nishadi, kamuwa da shan kodin nada tsananin hatsarin da zai iya kisa. Kamar saura abubuwan maye irinsu “opiates”, kokarin fita daga kangin shan kodin nada tsananin wahala hakan kan sa zaka ga matashi ya ci gaba da sha ba zai iya tsaya wa ba.

A shekarar 2017, majalisar wakilai ta bukaci hukumar NAFDAC, ta haramta sayar da kodin a kananan shagunan sayar da magani a fadin tarayyar kasar nan.

An kuma bukaci hukumar ta NAFDAC ta tabbatar da cewa, sai da takardar likita kawai za a iya sayen kodin a kuma samar da wani tsari da za a iya gane yawan mutanen da suke amfani da maganin domin gane wadanda suke sha maganin fiye da kima.

Bincike na baya bayan nan ya nuna cewa, gawamnatin tarayya ta kiyasta ana kwankwadar kwalba miliyan 3 na maganin tarin kodin a kullum a fadin Arewacin Nijeriya

Exit mobile version