An Fara Binciken Kone-konan Ofisoshin Hukumar Zabe Ta INEC

INEC

Daga Yusuf Shuaibu

Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin zabe ta fara gudanar da binciken musabbabin abubuwan da suka janyo lalata ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a fadin kasar nan. Haka kuma kwamitin zai binciki gobarar da ta tashi a ofisoshin hukumar zabe a fadin kasar nan.  Kwamitin zai gabatar da rahoto kafin makonni hudu a gaban majalisa domin daukan mataki.

Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da isassun jami’an tsaro a dukkan ofisoshin hukumar zabe a fadin kasar nan. Wannan ya zo ne bayan da dan majalisa mai suna Hon. Dachung M. Bagos ya gabatar da kudiri a kan farmakin ofisoshin hukumar zabe a fadin kasar nan. Majalisar ta bayyana cewa ci gaba da farmakin ofisoshin hukumar zabar a fadin kasar nan zai iya shafar harkokin zabe, jihohin da ‘yan ta’adda suka kone ofisoshin hukumar zabe dai sun hada da Akwa Ibom da Abia da Anambra da Imo da Borno da Ebonyi da Jigawa da Kano da Ondo  da Filato da Ribas da kuma Babban Birnin tarayya wato Abuja, wanda ‘yan ta’adda suka kone ofisoshin hukumar zabe guda 11 kurmus . Majalisar ta damu da yadda a cikin watanni 24 da suka gabata aka sami gobara a ofisoshin hukumar zabe 19. Majalisar ta yi matukar damuwa wanda ta bayyana cewa idan har ba a dauki matakan da suka kamata ba, hukumar zabe ba za ta samu isasshen ofishi da za ta gudanar da babban zaben shekarar 2023 a Nijeriya. Haka kuma ta bayyana damuwarta a kan yadda har zuwa yanzu ba a kama ko da mutum daya ba ballantana a gurfanar da shi a gaban kuliya bisa gudanar  da babban laifi.

 

Exit mobile version