Mustapha Abdullahi" />

An Fara Karbar Kudin Ajiyar Aikin Hajji A Kaduna

Aikin Hajji

Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Hajiya Hannatu Zailani ta bayyana cewa daga ranar Litinin ne hukumar ta fara karbar kudin ajiyar aikin Hajjin bana, wato na shekarar 2021, wanda ya yi daidai da 21 ga Disamba, 2020.

Bayanin hakan ya fito ne daga mai rikon mukamin shugabancin Hukumar, Hajiya Hannatu Zailani a lokacin wata tattaunawa da manema labarai a Kaduna.

Hajiya Hannatu ta kara da cewa, mai son zuwa aikin Hajjin na bana ana son ya fara ajiye kudi a kalla Naira 800,000 zuwa Miliyan 1.5 har ya zuwa lokacin da gwamnatin tarayya za ta fadi yawan kudin da za a biya domin zuwa aikin.

Daga nan Shugabar ta yi kira ga masu son tafiya aikin Hajjin da su ziyarci cibiyar yin rajistar da ta fi kusa da su a Kananan Hukumomin da su ke tare da fasfonsu, domin su karbi takardar da ta dace ta shaidar ajiyar kudi, domin yin rajista.

Hajiya Hannatu ta kuma ci gaba da yin kira ga maniyyatan da su hanzarta yin amfani da wannan damar domin yin ajiya a hankali.

 

Exit mobile version