A sashen gasar cin kofin zakarun Turai na Uefa Kama daga mako na sama daga ranar 16 ga wannan wata da muke cikin ne kungiyoyin da suka samu tikitin shiga gasar da suka hada da RB Liepzig da zata kece raini da kungiyar Liverpool sannan kuma kungiyar kwallon kafa ta PSG za ta fafata da Barcalona.
Ranar 17 ga wannan wata da muke cikin sa ne Fc Porto za ta kece raini da kungiyar Jubentus wadda dan wasa Cristiano Ronaldo yake jagoranta ya yinda Sebilla za ta fafata da kungiyar Borussia Dortmund
Kuma gaba dayan su masu horar da wadanan kungiyoyi, kama daga Julian Nagelsmann mai horar da RB Liepzig da Jurgen Klopp na Liverpool da Mauricio Pochetino na PSG da Ronald Koeman na Barcalona da Segio Conceicao na Fc Porto da Andrea Pirlo na Jubentus da Julien Lopetegui na Sebilla sai Edin Terzic daga Borussia Dortmund sun dauki hanyar ganin kungiyoyin sun samu nasarori a wannan gasa.
Itama kungiyar kwallon kafa ta Manchester City za ta buga wasan zagaye na biyu a gasar ta cin kofin zakarun turai wato Champions League da kungiyar kwallon kafa ta Borussia Monchengladbach ta kasar Jamus amma a kasar Hungary.
Borussia za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan farko a matakin gidanta ranar 24 ga watan Fabrairu a Fuskas Aarsena da ke Budapest a fafatawar kungiyoyi 16 da suka rage a gasar ta bana.
Shi ma wasan da Liverpool ya kamata ta fafata da RB Leipzig a Jamus za’a yi shi a Hungary sannan kungiyoyin biyu za su kara ranar 16 ga watan Fabrairu, sannan Liverpool ta karbi bakuncin wasa na biyu itama Manchester City za ta yi wa Borussia masauki a fafatawa ta biyu ranar 16 ga watan Maris a Ingila.