An Fi Samun Koma-bayan Kasuwancin Hatsi A Bana – Alhaji Magaji

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

 

Shugaban kungiyar masu awon hatsi na Jihar Neja, Alhaji Magaji Umaru ya bukaci gwamnati ta kara kaimi wajen samar da tsaro ta yadda manoma za su samu saukin wajen gudanar da harkokin noma.

Shugaban ya yi kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna farkon makon nan.

 

Shugaban ya ce kasuwancin hatsi a wannan shekarar an fi samun koma-baya musamman yadda mahara suka mamaye dazuka tare da hana wa manoma damar kusantar amfanin gonakinsu, wanda hakan ke kokarin tilasta tsadar abinci a jihar. Ya ci gaba da cewar duk da barazanar karancin ruwan sama da aka samu a damanar bana, manoma da suka samu damar tabukawa kuma na fuskantar kalubalen mahara wanda hakan ke tilasta abincin da aka samu yake kokarin lalacewa a gonaki ba rare da an kawo shi gida ba.

 

Ya ce wuraren da ake samun damar shiga dan sawo abinci ba hanya, wanda bisa tilas suke hakura da dan abin da ke shigowa, shi ya sa farashin abinci ya kasa saukowa duk da cewar an shiga kakar amfanin gona.

 

Da ya juya kan zargin da ake yi wa ‘yan kasuwar na boye abinci kuwa, ya ce ai ba dan kasuwar da zai so ware kudade dan juyawa ya yi tunanin sayen abinci ya boye dan tunanin ya yi tsada sannan ya sayar, dukkan kayan da ka gani nan rashin ciniki ne da tsadarsu ya sa ka gan shi a jibge haka.

 

“Dan haka, ina jawo hankalin gwamnati ganin tana da kudurin bunkasa bangaren noma ta taimaka wa manoma da kayan aiki kan kari ta yadda za su samu damar yin noman rani.

 

“Jihar nan Allah ya albarkace ta da kasar noma wanda kuma idan za a taimaka lallai za a iya noma sau uku a shekara, hakan ne zai saukaka tsadar farashin abinci,” in ji shi.

 

Exit mobile version