Mujallar kwallon kafar Faransa da ke bada kyautar gwarzon duniya ta Ballon d’Or, ta fitar da sunayen wasu fitattun ‘yan wasa a matsayin kungiya guda wadanda tace sun yiwa takwarorinsu zarra.
‘Yan wasan da mujallar wasannin ta kira da ‘tawagar Ballon d’Or’ sun hada da mai tsaron raga na kasar Rasha Leb Yashin, sai kuma Franz Beckenbauer na Jamus, Cafu na Brazil da kuma Paolo Maldini na Italiya a bangaren maso tsaron baya.
A bangaren ‘yan tsakiya kuwa, mujallar wasannin ta Faransa ta zabi Dabi Hernandez na Spain, da Lothar Matthaus na Jamus, ya yinda kuma a bangaren ‘yan tsakiya masu kai hari mujallar ta zabi Diego Maradona da kuma Pele.
Lionel Messi, Cristiano Ronaldo da kuma Ronaldo Nazario na Brazil ne suka mamaye bangaren masu jefa kwallo a tawagar ‘yan wasan mafi karfi ta ballon d’Or da mujallar wasannin Faransar tace sune gwanayenta.
Har ila yau a cikin jerin ‘yan wasan babu tsohon dan wasa Michel Platini na kasar Faransa sannan babu dan wasa ko daya daga nahiyar Africa ko Asia bugu da kari babu wani dan wasa da aka zaba daga yankin burtaniya.