Connect with us

WASANNI

An Fitar Da Jadawalin Yadda Za A Buga Gasar Carabao Cup

Published

on

Hukumar kula da gasar Carabao dake kasar Ingila ta fitar da jadawalin yadda za’a fafata wasannin zagaye na uku na gasar ta wannan kakar inda acikin jadawalin Liberpool zata fafata da Chelsea.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce dai ta lashe gasar a kakar wasan data gabata bayan ta doke kungiyar Arsenal a wasan karshe a babban filin wasa na Wembley dake kasar Ingila a watan Maris din wannan shekarar.

Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool dai ta lashe gasar sau takwas yayinda Chelsea ta lashe gasar sau biyar sai dai wasa na baya bayan nan da suka fafata a gasar shine na kusa dana karshe a shekara ta 2015 kuma Chelsea ce tasamu nasara a karawar.

Kungiyar manchester United wadda itama ta lashe gasar da dama zata fafata a gida da kungiyar kwallon kafa ta Derby County wadda tsohon dan wasan Chelsea da Ingila, Frank Lampard take koyarwa.

Ga Yadda Jadawalin Yake Na Zagaye Na Uku

West Bromwich Albion da Crystal Palace
Arsenal da Brentford
Burton Albion da Burnley
Wycombe Wanderers da Norwich City
Odford United da Manchester City
West Ham United da  Macclesfield Town
Millwall da  Fulham
Liberpool da Chelsea
Bournemouth da Blackburn Robers
Preston North End da Middlesbrough
Wolberhampton Wanderers da Leicester City
Tottenham Hotspur da Watford
Blackpool da Kueens Park Rangers
Eberton da Southampton
Manchester United da Derby County
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: