Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da takardar bayanin samun bunkasuwa mai dorewa a fannin sufuri ta kasar Sin a yau, inda aka bayyana ayyukan sufuri da nasarorin da aka samu a wannan fanni.
Takardar ta bayyana cewa, yanzu ana fuskantar babban sauyi a duniya, kasa da kasa suna da nasaba da juna, don haka sufuri yana da muhimmanci wajen kara mu’amala da juna, da sa kaimi ga sada zumunta a tsakanin jama’a. A matsayin wata babbar kasa mai sauke nauyinta, Sin ta aiwatar da ayyukan ajandar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030 ta MDD, da shiga ayyukan kyautata sufuri na duniya, da kara hadin gwiwa a tsakaninta da kasa da kasa don samar da gudummawarta wajen sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa a duniya da kuma neman raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. (Zainab)
Rayukan Amurkawa Na Fuskantar Babbar Barazana Sakamakon Tsarin Kiwon Lafiyar Kasar
A lokacin da cutar mashako ta COVID-19 ke ci gaba...