A yau Litinin ne, ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da takardar bunkasa sha’anin makamashi na kasar Sin a sabon zamani.
Takardar ta bayyana cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan sa kaimi ga yin kwaskwarima kan sha’anin makamashi, kuma an samu babban canji kan hanyoyin samar da makamashi da amfani da su, don haka an samu manyan nasarori kan raya sha’anin makamashi.
Takardar ta ce, yayin da ake tinkarar sauyin yanayi, da kalubalen kiyaye muhalli, da kayyade amfani da makamashi da sauran batutuwan duniya, Sin ta bi tunanin al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama, da sa kaimi ga canja tsarin raya zamantakewar al’umma tare da kiyaye muhalli, da shiga aikin sarrafa makamashi na duniya, da hada hannu da kasa da kasa wajen neman sabuwar hanyar samun bunkasuwa mai dorewa a fannin makamashi a duniya. Bunkasuwar sha’anin makamashi na kasar Sin a sabon zamani ta nuna goyon baya ga samun bunkasuwa mai dorewa a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’umma a kasar, kana ta samar da babbar gudummawa wajen samun isasshen makamashi, da tinkarar sauyin yanayi na duniya, da sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya. (Zainab)