Connect with us

JAKAR MAGORI

An Gano Bidiyon Wanda Ke Lalata Mace Cikin Motar Majalisar Dinkin Duniya

Published

on

Majalisar dinkin Duniya, ta ce ta kaddamar da wani bincike a kan wani bidiyo da ke yawo na mace da namiji suna jima’i a daya daga cikin motocinta a Isra’ila. Kakakin sakataren majalisar, Stephane Dujarric, ta sanar da manema labarai a New York cewa majalisar ta matukar girgiza kuma ta damu da bidiyon. Dujarric ta sanar da cewa, akwai yiwuwar wadanda suke jima’in an aiko su ne daga UN Truce Superbision Organization (UNTSO).

Gajeren bidiyon ya bayyana mace sanye da jar riga tana zaune a kan wani mutum da ke gidan baya a motar. A tare da su a cikin motar da ke tafiya akwai direba sai wani mutum daya mai sanko. Rahoton manema labarai ya nuna cewa an nadi bidiyon a titin HaYarkon. Amma kuma Majalisar dinkin Duniya ta ce ba ta da tabbaci a kan ingancin bidiyon.
Dujarric ya ce: “Mun ji matukar tsoro sannan al’amarin ya dame mu a kan bidiyon. “Bidiyon da muka gani abin ashsha ne, kuma ya take kokarin da muke yi na yakar rashin da’a a tsakanin ma’aikatan. “Mun gano bidiyon ne bayan kwanaki kadan da fitarsa, amma tuni muka sanar da ofishin bincikenmu don fara binciken da gaggawa. “Bincikensu na tafiya da sauri. Mun gano inda al’amarin ya faru amma akwai yuwuwar UNTSO ce ta ba su aiki.
An kusa kammala binciken, “Kamar yadda Majalisar dinkin Duniya ta saba, za a bayyana sakamakon binciken bayan kammala binciken sannan a dauki mataki”
Kamar yadda majalisar ta bayyana, UNTSO na da hedkwata a kasar Jerusalem kuma su ne kungiya ta farko da suka je kwantar da tarzoma wacce Majalisar dinkin Duniya ta kafa a 1948. Ta tura ma’aikatan da suka hada da masu lura da rundunar soji don tsagaita wuta, duba yarjejeniya a kan makamai da kuma kiyaye sake barkewar rikici.
A wata takarda, UNTSO ta ce ta shirya tabbatar da yaki da rashin da’a da suka hada da cin zarafi ta hanyar jima’i. Tana tunatar da jami’anta hakkin da ke kanta kamar yadda Majalisar dinkin Duniya ta wajabta musu. Amma kuma Ms Heather Barr, daya daga cikin daraktar kare hakkin mata ta majailsar, ta ce bidiyon kwata-kwata bai ba ta mamaki ba.
Advertisement

labarai