Wani sabon rahoto da aka fitar a ranar Laraba ya bayyana cewa, tsohon gwarzon dan kwallon duniya na Argetina, Diego Maradona ya mutu ne sakamakon cututtkan da ke da nasaba da koda da hanta da kuma zuciya sabanin kwankwadar barasa da muggan kwayoyi da aka bayyana da farko.
Binciken da aka gudanar kan gawarsa, bai gano wata alamar barasa ko muggan kwayoyi tattare da marigayin ba kamar yadda mai shigar da kara na gwamnatin Argentina ya bayyana a gaban kotu.
A ranar 25 ga watan Nuwamban da ta gabata ne, Maradona wanda ya jagoranci kasarsa wajen lashe mata kofin duniya a shekarar 1986 a Medico, ya mutu yana da shekaru 60 bayan yasha fama da rashin lafiya a lokuta da dama kafin mutuwar tasa.
An yi wa gawarsa gwaji ne don kawar da shakkun kan musabbabin mutuwarsa kodayake tsohon gwarzon kwallon duniyar ya sha fama da kwankwadar hodar iblis da barasa a lokacin rayuwarsa duk da cewa likitoci sun nuna masa illar yin hakan.
Sa dai wata babbar kotu a birnin Buenos Aires dake kasar Argentina ta wanke likitan, Leopoldo Lukue, likitan da ya yiwa Maradona aiki bayan da tun farko ‘ya’yan mamacin suka zargi likitan da yin wasa da lafiyar mahaifin nasu.
A ranar Litinin din data gabata aka fara zaman kotun inda aka zargi likitan da yin sakaci wajen mutuwar tsohon tauraron kwallon kafar duniyar kuma tuni ya gurfana a gaban wata kotu dake Argentina domin amsa wasu tambayoyin da suke da alaka dashi.
Masu gabatar da kara a garin San Isidro kusa da birnin Buenos Aires sun sanar da cewar ‘yan Sanda sun kai samame asibiti da gidan likita Leopoldo Lukue domin tattara wasu shaidu kafin su gabatar a gaban kotu.
Binciken ya biyo korafin da ‘ya’yan Maradona guda uku suka gabatar da suka hada da Dalma da Giannina da Jana sakamakon irin kulawar da likitan ya baiwa mahaifin su lokacin da ya gamu da bugun zuciya.
Lukue wanda yaki cewa komai kan tuhumar da ake masa, ya wallafa hotan sa da na Maradona lokacin da ya bar asibiti ranar 12 ga watan daya wuce, kwanaki 8 bayan yi masa aiki a sibitin da yake duba dan wasan.
Marigayin yasha fama da jinya a ‘yan shekarun baya inda ko a shekarar data gabata sai da akayi masa aiki sakamakon kiba da yayi kuma take hanashi gudanar da wasu ayyukansa musamman na koyarwa sai dai daga baya ya warke kuma ya koma ya ci gaba da aikin koyarwa a kasar Medico kafin daga baya ya ajiye aikin ya koma gida Argentina sakamakon jikinsa yayi nauyi baya iya motsi sosai.
A matsayinsa na daya daga cikin shahararrun ‘yan kwallon kafar duniya, Maradona shi ne kyaftin na Argentina lokacin da ta lashe Kofin Duniya a shekarar 1986, inda ya buga wasa mai kayatarwa.
Maradona ya buga wasa a kungiyar Barcelona da Napoli lokacin da yake kan ganiyarsa, inda ya lashe Kofunan Gasar Serie A da kungiyar kwallon kafar ta Italiya sannan ya zura kwallo 34 a wasanni 91 da ya buga wa Argentina, inda ya wakilci kasar a gasar cin Kofin Duniya sau hudu.
Maradona ya jagoranci kasarsa a shekarar 1990 inda suka kai wasan karshe a kasar Italiya, ko da yake sun sha kashi a hannu Yammacin Jamus, amma ya sake jagorantarsu zuwa Amurka a 1994, sai dai an kore shi saboda samunsa da laifin shan kwayoyin kara kuzari.
Lokacin da ya komo karo na biyu domin sana’arsa ta kwallon kafa, Maradona ya sha fama da jarabar shan hodar ibilis kuma an haramta masa buga wasa tsawon wata 15 bayan gwajin da aka yi masa a shekarar 1991 ya nuna cewa yana shan kwayoyi.
An rufe Maradona kusa da mahaifansa a makabartar Bella Bista da ke wajen Buenos Aires sai dai an samu turmutsutsi, bayan da dubban mutane suka yi jerin gwano don ganin gawar a fadar shugaban kasa.
Daga karshe sai da ‘yan sanda suka bada hayaki mai sa hawaye, su ka kuma canza wa akwatin gawar Maradona wuri, bayan da jama’a suka balla kofar dakin da ta ke ajiye ta don yi masa ganin karshe.
An haifi Diego Armendo Maradona ranar 30 ga watan Oktoba na shekara 1960 wato ya mutu kenan ya na shekaru 60 da haihuwa, kuma an haife shi a wani gari mai suna Lanus dake karkashin mulkin babban birnin Buenos Aires.
Maradona ya na daya daga cikin yara hudu da iyayensa suka haifa.Tun ya na dan shekaru 11 a duniya a fara daukar hankalin jama’ar kasar Argentina game da irin hukumomin kwallo da ya lakanta, saboda haka wani mai koyar da ‘yan wasan Argentina ya dauke shi a cikin kungiyar kwallon yafa kanana ta kasar da ake kira Cebollitas.
Maradona yana da shekaru 12 ya taba yin hira da wai gidan Talbijin inda ya ce shi burinsa a duniya shine idan ya girma ya halarci gasar cin kofin kwallo ta duniya tare da kungiyar kwallon Argentina kuma ya dauko kofi.
A lokacin da ya cika shekaru 16 a duniya ya shiga kungiyar kwallon matasa ta kasa, inda ya zama jagoran ‘yan wasan kuma daga lokacin daya shiga wannan kungiyar har ya fita ba su taba cin wani kofi ba na kasa da kasa, amma ya saka kwallaye a raga har sau 115 a cikin wasanin 166 da ya buga.