A zamanin yanzu a duniya da ake amfanin da zanen tafin hannu a wajen bayanan kimiyyar kere-kere, rashin samun wannan tambarin zane baiwa ce ko akasin haka? Wannan mazajen dangin Sarker ne kawai za su iya tabbatarwa.
Shekaru da dama da suka gabata har zuwa yau ana haifar maza a dangin Sarker da ke kasar Bangaladash ba zanen tafin hannu, kuma hakan ba zai zama wata babbar matsala ba a karni daya zuwa biyu da suka gabata, amma a wannan zamanin na yau, lokacin da ake amfani da zanan hannu a matsayin babbar hanyar gano mutane, wannnan matsala ce babba.
Misali, wasu daga cikin mazajen dangin na Bangladesh sun kasa samun lasisin tuki saboda rashin zanen yatsun hannu, yayin da wasu kuma suka yi jinkirin yin tafiya saboda tsoron samun matsala a filayen jirgin sama, saboda wannan dalili.
“Na biya kudi kuma na ci jarrabawar, amma ba su ba ni lasisi ba saboda ba zan iya samar da zanan yatsan hannu ba. Wannan al’amari ya sha jisga ni a gaban mutane,” in ji Amal Sarker.
Amal ya kara da cewa, akoyaushe yana dauke rasit na lasisin tuki yayin tuka babur dinsa, amma hakan bai taimaka ma sa ba lokacin da ‘yan sanda suka tsayar da shi. Idan aka sayar da shi, yana nuna masu rasit din da kuma santsin tafin hannunsa, amma jami’an ‘yan sandan ba su taba barin sa babu kadin bele ba.
Siyan katin SIM yana zama matsala ga maza a dangin Sarker, tunda gwamnatin Bangaladash ta gabatar da doka don sharadin siyan katunan SIM ta hanyar daidaita zanan yatsan hannu tare da rumbun adana bayanan kasa. Ba tare da zanan yatsan hannu ba, Apu da Amal Sarker sun kasa samun katin SIM din su, kuma yanzu duka suna amfani da katunan da aka saya da sunan mahaifiyarsu ne.
Mazaje a cikin dangin Sarker, daga gundumar Rajshahi, a arewacin kasar Bangladesh, suna fama da wani yanayi mai saurin gaske wanda ake kira ‘Adermatoglyphia’. Hakan ya zama sananne abu ne a 2007, lokacin da Peter Itin, wani likitan fata na kasar Switzerland, ya jagoranci wata matashiya ‘yar kasar Switzerland da ke fama da matsalar shiga Amurka, saboda ba ta da zanan yatsu. Fuskarta tayi daidai da hakan a fasfot dinta, amma yatsun hannunta sun kasance masu santsi.