An gano karin gawarwaki uku daga ragowar ashirin da shida (26) wadanda jirgin ruwa ya kife a ranar Lahadi a kauyen Kojiyo da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto, a ranar Talata.
Wata majiya mai tushe ta ce, masunta ne suka gano gawarwakin a yammacin ranar Talata a wurare uku daban-daban.
- NNPP Za Ta Iya Goyon Bayan Takarar Tinubu A 2027 – Sakataren Jam’iyyar
- Ronaldo Ya Samu Kyakkyawar Tarba A Hong Kong
“A yayin da ake ci gaba da neman karin gawarwakin mutanen da hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a ranar Lahadin da ta gabata, an gano gawarwaki uku.
“Masunta ne suka gano gawarwakin uku a wurare daban-daban da suka hada da Kojiyo, Bare da kuma wani kauye a karamar hukumar Wurno, a yayin da suke aikin ceto gawarwakin inda reshen bishiya ya sargafe gawarwakin,” inji majiyar.
An Sallaci gawarwakin tare da birne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.