Connect with us

LABARAI

An Gano Yadda Dasuki Ya kulla Zumuncin Buhari Da Tinubu

Published

on

An bayyana cewa, tsohon Mai Bai Wa Shugaba Goodluck Ebele Jonathan, shawara kan harkokin tsaeon kasa, Kanar Sambo Dasuki, ne ya fara gabatar da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ga tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma Jagoran Jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu a shekara ta 2011 gabanin su yi hadakar zabe tsakanin rusassun jam’iyyunsu na CPC da ACN.

daya daga cikin wadanda su ka assasa tsohuwar jam’iyyar Shugaba Buhari ta CPC, Dr. Ahmed Kurfi, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da jaridar Sunday Sun ta yi da shi ranar Lahadin da ta gabata.

Ya kara da cewa, lamarin ya faru ne gabanin zaben 2011, inda sai bayan shekara guda da hada wannan zumucin ne, tsohon Shugaba Jonathan ya gayyaci Kanar Dasuki mai ritaya ya nada shi mukamin mai ba shi shawarar a ranar 22 ga Yuni, 2020.

Kurfi ya ce, tare da shi da Dasuki da Ministan Ilimi ba yanzu Adamu Adamu da Mawallafin jaridar Daily Trust Kabir Yusuf da kuma tsohon Shugaban Kamfanin Dillanci Labarai na Nijeriya (NAN) Wada Maida su ka ziyarci Tinubu din gabanin Babban Zaben 2011.

Ya ce, “Ina tsaka kace-kace a hadin gwiwar CPC da ACN, wacce daga bisani ta rikide ta zama APC. Ni ne na jagoranci tawagar da ta je a gana da Tinubu.”

Ya cigaba da cewa, “gaskiyar magana ita ce, Sambo Dasuki ne ya gabatar da mu ga Tinubu, saboda sun yi zaman gudun hijira tare da shi a lokacin da Abacha ya ke farautar su.”

Da ya jaddada irin yadda Dasukin ya yi fafutuka ga Shugaba Buhari a siyasance, Dr. Kurfi ya kara da cewa, shi ne kuma ya bukaci tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya bai wa Buhari kudin da ya yi yakin neman zabe da su.

Don haka sai ya ce, akwai kyakkyawar alaka tsakaninsu a siyasance, duk da cewa, bayan Buhari ya hau mulki, ya daure Dasuki ne, inda kara da cewa, ya na tsammanin cewa, wannan sabanin da ke tsakaninsu ya samo asali ne tun a lokacin aikinsu na soja, amma ba a lokacin siyasa ba.

“A fili ta ke cewa, duk yakin neman zaben da mu ka yi a rusasshiyar Jam’iyyar APC tare da Sambo da a ka yi. Sambo ne ya fara kirkirar ganawar da a ka yi da Tinubu. Sambo ne a tsakani. Shi ne ya tsara komai, kuma lokacin da mu ka sauka a Legas ma shi ne ya yi ma na dukkan shirin da su ka dace,” in ji shi, ya na mai cewa, “ka san Sambo ya san mutane sosai. Idan ka na so ka san mutumin da ba shi da kabilanci a Nijeriya, to ka nemi Sambo. Za ka gan shi ya shaku kowanne dan Nijeriya ba tare da la’akari da yarensa, addininsa ko wani abu ba.”

Idan dai za a iya tunawa, jim kadan da hawan mulkin Shugaba Buhari a 2015 bayan faduwar gwamnatin Jonathan, gwamnatinsa ta garkame Dasuki, inda ya shafe kimanin shekara hudu a tsare ya na fuskantar shari’a bisa zarge-zargen da su ka hada da kudaden cinikin makamai, kafin daga bisani a bayar da belinsa.

Kan hakan Dr. Kurfi ya nesanta sabanin Buhari da Dasuki da tarihin siyasarsu, ya na mai cewa, watakila batun ba zai rasa nasaba da tun lokacin da su ke aikin soja ba.

“Ka san halin zamantakewar gidan soja, kamar yadda Adamu Ciroma ya sha fada a wasu hirarrakinsa. Ya kan ce, su na cewa, Buhari Buhari ya na da riko. Idan ba haka ba don me ba zai yafe ba? Shi ne ya yi wa zababbiyar gwamnatin dimukradiyya juyin mulki kuma ya daure Shagari. To, meye za ka yi korafi, don wadanda ka yi amfani da su a ka yi wa Shagari juyin mulki su ma sun juye ka?

Idan za a iya tunawa, an bayar tarihi a wani littafi mai suna ‘An Encounter with the Spymaster’, wanda Yushau Shuaib, ya rubuta cewa, Dasukin ya taba durkusa wa a gaban tsofaffin gwamnonin jihohin Lagos da Osun, Tinubu da Bisi Akande, ya na rokon su kan su yarda su amince da Buhari a matsayin dan takarar masalaha na jam’iyyun ACN da CPC a Babban Zaben 2011.

Littafin ya kara da cewa, abinda ya hana Buhari lashe zaben 2011 shi ne, yadda ya ki yarda da mataimakinsa na yanzu, Yemi Osinbajo, a matsayin Mataimakin Shugaban kasa, ya je ya jajubo Tunde Bakare, lamarin da ya sanya jiga-jigan siyasar yankin na Yarabawa janye jikinsu daga takarar.

Haka nan shi ma tsoho Dogarin Buharin a lokacin da ya ke Shugaban Gwamnatin Mulkin Soja kuma tsohon Sarkin Gwandu, Alhaji Mustapha Jokolo, ya taba cewa, Dasuki ya taka rawa mai yawa wajen ganin an kifar da gwamnatin Shagari, don a kafa gwamnatin mulkin soja ta Janar Buhari a 1983.

Yayin da Kurfi ya juya kan batun yadda a ka kafa Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya a halin yanzu da kuma rikicin da ta ke fuskanta na cikin gida, ya ce, ai da ma ba cikakkiyar jam’iyyar siyasa ba ce, illa dai kawai mabukata masu neman mulki ko ta halin kaka ne su ka taru su ka kafa ta.
Advertisement

labarai