Daga Mustapha Abdullahi,
Domin a samu ingantacciyar rayuwa ga kowa, ya zama wajibi ‘yan Nijeriya su hanzarta yin watsi da batun bambance-bambance a tsakaninsu, musamman na kabinlanci ta hanyar yin amfani da kalaman da ba su dace ba.
Wani dan kasuwa, wanda ya yi takarar Shugabancin kasar nan a shekarar 2019, Mista Gbenga Olawepo- Hashim ne ya bayar da wannan shawarar a zantawar da namema labarai a Kaduna cikin makon nan.
Da yake magana game da irin yadda ake samun batutuwan rabe-raben kawunan jama’a a kan kabilanci a Nijeriya, Hashim ya bayyana cewa yin maganganu a kan wata kabila ana dora mata laifi a kan wata domin kawai a sanya wasu su rika yin ramuwar gayya, ba zai haifar wa kasar da mai ido ba, don za a iya samun lalacewar al’amura.
Ya ce, “duk mai son Nijeriya lallai zai damu kwarai. Ni na damu, dukkanmu muna da abin da za mu iya yi, shugabannin al’umma da kungiyoyi masu zaman kansu ya dace su yi dukkan mai yuwuwa a samu mafita.”
“Yanzu lokaci ya yi da za a kara karfafa wa Hukumomin tsaro domin su aiwatar da aikinsu kamar yadda ya dace. Kuma yanzu lokaci ne da shugabannin za su yi aikin da zai nuna cewa lallai su shugabanni ne. Dole mu hada kai domin mu kubutar da kasa”, in ji Olawepo – Hashim
Shahararren dan kasuwar ya bayyana cewa, “shugabanni a kowane irin mataki dole su kauce wa yin kalamai da aiki a aikace da zai nuna goyon baya ga duk wani bangare game da tashin-tashina, domin zai iya haifar da matsala a batun zama kasa daya al’umma daya da kuma harkar tsaro.
Ya ce, “a kan matsalar fadace-fadace a tsakanin Makiyaya da Manoma a ko’ina a fadin Nijeriya kuwa, dukkan ‘yan kasa nagari da suka hada har da shugabanni sun amince duk wani lamari na kiwo da zai iya haifar wa wani matsala a kan kasuwancinsa ko harkarsa, to a bar shi domin a yi amfani da hanyoyin zamani a samu ci gaban da kowa ke bukata”.Ya bayyana wadansu wurare da akwai ainihin batu a bayyane na dai- daitawa a tsakanin Juna na kirkiro da yan sandan Jihohi da kananan hukumomi da suke tafiya kafada da kafada da Yan sandan Gwamnatin tarayya da nufin kara karfafa harkar aikin dan Sanda ta inganta kuma a samu karin ingantawar harkokin tsaro da dai sauransu.