Ammar Muhammad" />

An Gaza Dakile Zanga-zangar Riguna Masu Ruwan Dorawa A Kasar Faransa –Gwamnati

Rahotanni sun bayyanawa cewa; gwamnatin Faransa ta amince cewar matakan tsaronta sun gaza wajen dakile tarzomar da wani gungun masu rigunan dorawa suka tayar a karshen mako a birnin Paris, inda suka kone shaguna da dama, tare da sace dukiya mai tarin yawa.

Tarzomar da ta haddasa arrangama tsakanin gungun masu rigunan dorawar da jami’an tsaro ta auku ne a yankin Champs Elyssee da ke birnin Paris a ranar Asabar, yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaban Macron karo na 18, wadda aka saba yi a kowanne karshen mako.

Gidan Rediyon Faransa sun labarto cewa; a wannan karon masu boren sun buwayi ‘yan sanda saboda yawansu, abinda ya basu damar satar dukiya daga shaguna akalla 80, tare da cinnawa wasunsu wuta, a takaice dai jami’an tsaro basu shawo kan lamarin bai sai bayan kusan sa’o’i 7.

Hakan tasa Firaministan Faransar Edouard Phillippe, ya bayyana cewa tabbas lamarin ya nuna cewa hukumomin tsaron kasar sun tafka wasu kura-kurai wadanda tilas a gaggauta gyarawa.

Tun a jiya Lahadi, shugabannin masu sanye da rigunan dorawa da ke zanga-zangar adawa da manufofin shugaba Macron, suka bukaci ministan cikin gidana Faransa Christophe Castaner yayi murabus saboda gazawar gwamnati wajen kare dukiyar al’umma, inda kuma suka nisanta kansu da gungun masu masu tarzomar.

Exit mobile version